Home » Daga yanzu duk wanda ka gani da shaidar tantancewa a twitter biya yayi

Daga yanzu duk wanda ka gani da shaidar tantancewa a twitter biya yayi

Kamfanin twitter sun kasance a baya suna bada shaidar tabbatar wa ga sanannu mutane da sauran shahararrun masu amfani da kafar na twitter,in duk wanda ya cika kaidar su yake samun wannan shaidar a kyauta.

Sai dai tun bayan da Elon Musk ya sayi amfanin na twitter, ya ta zuwa  da sauye sauye daga ciki ne har ya kawo tsarin da zai bawa kowa daman mallakar alaman tantan cewa ta hanyar biyan wasu kudade duk wata.

A baya anji shi yana cewa babu amfani bawa wasu shaidar haka kawai a kyauta, inda ya nuna cewa zai kwace dukkan wani shaida da aka bayar a baya, duk mai bukata sai dai ya biya kudi kaman yanda masu bukata suke biya a yanzu.

Yanzu dai kamfanin ya fitar da sanarwan dake nuni da cewa daga daya ga watan Afrilu duk wanda ka gani da shaidar tantancewa a twitter biya yayi, domin zasu soke shaidar da suka bayar kyauta a baya duka.

Related Posts