Home » The North (Arewa)

Yanzu kusan kowa ya fahimta, ICT jigo ce ga duk mai rayuwa a ƙarni na 21; ba wani sashe, aiki ko sana’a da fasahar zamani ba ta shafa ba a yau. Kuma, matuƙar kana buƙatar komai naka ya tafi maka daidai a yau, wajibi ne ka nemi ilimin fasahar zamani, daidai gwargwadon buƙatarka na abubuwan da suka shafe ka.

Wannan ya sa wasu haziƙan matasa daga Arewacin Nijeriya, masu kishi da son bunƙasa harkokin fasahar zamani da kimiyya a yankin Arewacin Nijeriya, suka ƙirƙiro wata tafiya, mai manufa guda, don bada gudunmawa da taimakekkeniya musamman ga matasan Arewa, don cike giɓi (gap) na tazarar da aka bar mutanen Arewa musamman a ɓangaren fasaha.

Domin gudanarwa bisa tsari, akwai kwararru (mentors) za su riƙa wayar mana da kai, da sanar da mu duk wasu damarmaki da za mu samu don gina kanmu, dogaro da kai da buƙansa kasuwancinmu da fasahar zamani daidai da ƙarni na 21 cikin harshen Turanci da harsunanmu na gida (Hausa, Fulfulde, Kanuri da sauransu).

The North na da ‘groups’ a Facebook (The North) da Telegram . Akwai shafuka a Twitter (@TheNorth1920) da Podcast (The North), akwai kuma Channel a Youtube don bibiya da ƙaruwa da abubuwa da za ana wallafawa.

The North, ba wai iya tafiya ce ta koyarwa ba kaɗai, a’a, tafiya ce da za ta taimaka mana don mu gina kanmu, har muna samun kuɗaɗen shiga da Freelancing, Digital Marketing, Blockchain Technology, Digital Creativity…

Kindly join #TheNorth as a ‘mentor’ or ‘mantee’, each one of us can make a difference, but together we can make change.

✍️ Aliyu M. Ahmad
26th Safar, 1444AH
3rd September, 2022CE

Related Posts