Home » Airtel Nigeria sunyi sabon MD/CEO

Airtel Nigeria sunyi sabon MD/CEO

Kamfanin Airtel Africa Plc ya sanar da nadin Carl Cruz a matsayin sabon manajan darakta kuma shugaban kamfaninsu na Airtel Nigeria.

A ranar Alhamis, kamfanin sadarwa ya sanar da cewa Cruz zai karbi sabon aikinsa a ranar 5 ga Mayu, inda zai gaji C Surendran.

A cewar sanarwar, Cruz, wanda ya yi digirinsa na farko a fannin harkokin kasuwanci a jami’ar De La Salle ta kasar Philippines, zai kasance cikin  kwamitin zartarwa na Airtel a matsayin daraktan gudanarwa zai kuma rika mika rahoto ga Segun Ogunsanya, babban jami’in gudanarwa (Shugaba). , Airtel Africa Group, da kuma hukumar gudanarwar reshenta, Airtel Nigeria.

A baya, Cruz ya rike mukamin shugaba da darekta a Unilever Sri Lanka. Ya kuma rike mukaman jagoranci a Unilever Philippines da Hindustan Unilever India.

Related Posts