Home » Startup Kano sun shirya koyarwa na musamman ga mata 20 

Startup Kano sun shirya koyarwa na musamman ga mata 20 

A cigba da aiyukan wayar da kai da kuma horas wa akan fannoni daban daban da Startup Kano suke yi don ganin sun taimakwa Al`umman Arewa wajen samun cin moriyar fasahar zamani tare da bunkasa kasuwancin su. 

Sun samar da wani shiri na musamman da suka kira da PitchStar, inda suke koyar da matasa masu Startup hanyoyin da zasu bi wajen inganta Startup nasu tare da basu shawari da zai taimaka musu.

A wannan karon Startup Kano da hadin guiwar Women Founders Group sun shirya koyarwan ne wa mata masu kana nan kamfanonin dasu ke arewacin Nijeria.

wasu daga mahalarta taron

Domin koya musu dabarun kasuwanci,za ayi tsawon mako biyu ana koyar dasu darrusa da suka shafi startup da kuma kana nan sanaoi, da zasu iya yi domin dogaro dakai.kaman yanda Startup Kano suka wallafa a shafin su na Twitter.

Related Posts