Home » Apple sunyi babban taron su na WWDC 22 

Apple sunyi babban taron su na WWDC 22 

WWDC taro ne da kamfanin Apple inc suke shirya wa duk shekara inda suke baje kolin sabbin fasaha da suka tanadar wa masu mu`amala da kayan kamfanin na Apple,a wannan shekarar sunyi taron ne a yanar gizo inda aka fara tun ranar shida ga watan yuni.

Mun duba wasu daga cikin muhimman abubuwa da suka faru a wurin wannan taron nasu, ga kadan daga abubuwan da suka gabatar.

ios 16 

Manhajan Apple na ios 16 na daya daga cikin abunda kamfanin suka yi bayani akai tare da nuna yanda tsarin manhajan zai kasance, sabon manhajan yazo da tsare tsare masu yawan gaske wanda a baya babu su,akwai chanji a yanda wayan zai kasance in yana rufe(lock screen),akwai kuma tsarin live activity wanda zai baka daman yin wasu aiyuka da wayanka kohda yana rufe.

Bangaren widget shima an samu cigaba sosai da kuma wasu chanji da aka kawo,iMessege shima an kawo tsarin da zai baka daman sake gyara sako bayan ka tura zaka iya kuma goge sakon gaba daya bayan ka tura,sun kuma kawo tsarin tura hoto yanzu zaka iya sharing photo library kaman yanda ake yi a google photos yanzu zaku iya da iCloud a tsabon tsarin da aka kawo.

Sabon computer MackBooks

Sabon computer kamfanin Apple MackBook Air  na daga cikin jerin abunda akayi bayani akai inda aka bada sanar wa cewa sabon computer zaizo da tsarin M2 chip, shekara biyu kenan yanzu bayan da aka fitar da computer su mai aiki da M1 chip yanzu an tafi M2, tsarin sabon computer zaizo ne a inchi 13.6 na display wanda retina liquid ne, akwai kuma touch Id a magic keyboard na computer din zai zo kuma da wurin USB-C guda biyu, akwai kuma Thunderbolt port wanda za iya amfani da shi a hada da Monita,yana kuma da tsarin saurin yin chaji zai iya zuwa 50% a minti talatin.

Mac Os 

Manhajan Computer (OS) na Mac shima an gabatar da sabo wanda zaiyi aiki a laptop na Apple tsabon tsarin da macOs Ventura yazo dashi ya hada da Stage manager tools akwai kuma update na Spotlight,Mail,da Safari.

Tsarin Karban Bashi kayan Apple 

Kamfanin sun sanar da sabon tsari da zai baya masu aiki da Apple daman karban bashin abunda suke so daga kamfanin na Apple inda zasu biya wani bagare na kudin a take sauran kuma su biya  a cikin mako shida inda a duk bayan mako biyu za`a rika biya, mutum zai biya sau uku kenan cikin mako shida.