Home » Bakon mu na mako 

Gabatarwa

Sunana Ismail Waziri, kuma an haifeni ne a unguwan Pantami dake garin Gombe. Nayi karatun firamare da na sakanderiyal duka a makarantar; Alheri Model High School, dake Garin Gombe. Baici nan da na gama sai na garzaya Colleji na kasa wato; Federal college of Education (Technical) Gombe, inda nayi karatun computer na dan karamin zango domin samun takardar shaida na cewa na iya amfani da na’ura mai kwakwalwa wato Computer. Daga nan kuma sai na garzaya Jami’an kasa dake garin Kashere, a Jihar Gombe inda na karanta kimiyyar na’ura mai kwakwalwa wato; B.sc. Computer Science. Wannan kadan kenan daga cikin karatuttukan danayi, duba da cewa dukka sauran nayisu ne a yanar gizo kuma dan ci gaban kaina bawai don samun takarda ba. 

Me ya ja ra’ayinka ka shiga Harkan Tech?

Tun ina aji uku (3) a sakanderiyal da na mallaki na’ura nakaina na farko, hakan yasa na fara jin sha’awan nima ace ina kirkiro fasaha wanda mutane zasu rika amfani dashi, wanda hakan yasa tun a lokacin nafara hallartan shagon harkoki na yanar gizo na kawuna, wato; Internet Cafe. Inda nazama yaronshi na farko bayan budewa, nayi hakan ne don insamu korewa akan abubuwa daban daban da ya shafi na’ura mai kwakwalwa. Daga nan sai na fara sha’awan karanta kimiyyar Na’ura a jami’a. 

Wasu kalubale ka fiskanta?

Alal hakika na fiskanci kalubale daban daban, musamman abunda ya shafi karatuna saboda wani sa’in zantafi taro na abunda yashafi kimiyyar na’ura da wato (Conference) wanda za ayi karatu bana makaranta, wani lokacin haka zan rasa gwaji, wato; test. Rashin kudi yana daya daga cikin kalubalen da na fiskanta saboda dalibi dai kowa yasan ba isheshen kudi gareshi ba. Wani sa’in sai na nemi Aron kudi inyi tafiya taro (Conference) da sauransu. To amma hakan baisa na sare ba, saboda ni nasan abinda nakeso in cimma. Mutane dayawa sunamin kallon ban san me nakeyi ba saboda tunanin kowa shine mutum yagama jami’a akan lokaci yayi bautan kasa yasamu aikin gwamnati. To amm samun karfin gwiwa danayi daga wurin iyayena na daya daga cikin abunda ya karamini karfin gwiwa. 

Wasu nasarori aka samu?

To Alhamdulillah, babban nasara dai shine a yanzu da kaina na dogara ba da gwamnati ko wani ba. Inada kananan kamfanoni na kimiyyar na’ura (Startup) wanda wasu an sansu, wasu kuma ni nasan kayana. Banda wasu kananan kasuwanci da nake tabawa a gefe wanda suke tallafa wa rayuwana na yau da kullum, saboda su wadancan kamfanoni (Startup) ba abune da zai fara kawo kudi yanzu yanzu ba.  Daya daga cikin nasaran da na samu shine, sanin mutane danayi wato Al’ummar da ake gwagwarmaya tare (Ecosystem). Hakan yasa na samu sanuwa nima a Nigeria da ma sauran kasashen duniya da kamfanoni na kimiyyar Na’ura duka. 

Ismail Waziri
Ismail Waziri da Ministan Sadarwa

Shawara ga masu bukata shiga Harkan fasaha.

Shawara na anan shine, duk wani wanda yake da sha’awan shiga harkan fasaha shine; da ya nitsu, ya fahimci abunda zuciyarshi takeso (passion) sannan kuma yayi tunani mai zurfi tare da bincike na kwarai (research). Sannan kuma sirrin shine magance matsala a ko ina a fadin duniya. Ba azo ayita gasa da juna akan abu daya ko don nuna iyawa ba. Kawo  mafita (solution) akan matsalar da take damun mutane (problem) shine nasaran mutum. Shi kimiyya  bawai hada wani babban abu bane, a.a duk kankantan abu indai zai magancewa mutane matsala, to bukata ya biya kuma mutum zai ci nasara. Sannan mutane zakaji suna ta yayata maganan samun kudi da ake a Tech, yakamata mu gane babu wanda zai mutu sai yaci iya arzikin da Allah ya rubuta mishi zaici, kawai dai dole mu jajirce sabida shima hakan ibada ne.

To abunda nayi magana akan wannan shine, mutane da dama don kudin suke shigowa harkan tech ba don cigaban kansu da kuma kasa ba, to indai hakan ta kasance mutum zaizo bai samu kudin ba kuma bai taimakawa kasa ba. A karshe ina kira ga matasa yan uwana da mu jajirce, wannan lokaci da ake samun sabbin fasaha sunata bayyana a duniya, lokaci ne da ya kamata mu shigo ciki a dama damu, muga me zamu iya yi don mu taimaki kasarmu kuma musamu arziki matuka. Musamman a kasa irin Nigeria da mukeda matsaloli dayawa, hakan dama ne ga masu kirkira (innovators) da su kirkiro abubuwan dasu magance matsaloli a fannin tsaro, kiwon lafiya, noma da kiwo, sufuri da dai sauransu. Allah ya bamu sa’a kuma Allah ya albarkaci neman mu.

Related Posts