Home » Bakon mu na mako 

Bakon mu na wannan makon daya ne daga cikin masu ruwa da tsaki a harkan fasaha a Arewacin Nigeria,wanda yake bada gudunmawa sosai a harkan fasaha.

Gabatarwa.

Assalamu Alaikum Sunana Ishaka Usman Idris an haifeni a garin Jos, a yanzu ina da zama a Lafiya jihar Nasarawa.Nayi karatu Primary da secondary zuwa Jss2 a garin Jos daga bisani aka yiwa Mahaifin mu chanji wurin aiki zuwa Lafiya Jihar Nasarawa anan na karasa Karatun secondary na shiga jami’ar Nasara State Dake keffi inda na karanci Geography na kammala kuma nayi bautan kasa.

Usman yana jawabi DEvfest

Me ya ja ra’ayinka ka shiga Harkan Tech?

Abunda ya jawo hankalin na koh ra’ayi na zuwa Harkan fasaha tech,a lokacin da muke secondary a 2007 zuwa 2008 akwai Application da muke aiki dasu wajen Chanja fasalin wasu Application din misali yanda muke Chanja logon opera mu saka namu,koh mu chanja sunan zuwa sunan mu irin wannan abubuwan da mukeyi yana mana daɗi kuma dai ya buɗe mana ido sosai kuma shine ya fara jawo hankalin mu akan abinda ya shafi fasaha domin yana min daɗi ta yanda muke Chanja abubuwa muna turawa abokan mu a wayoyinsu na Java da kuma symbian a wanchan lokacin.

Bayan haka tun ina yaro gaskiya Ni irin mai son kimiya ne inason kimiya inason buga game,duk wani abu da zanga ana amfani da na’ura yana burgeni sosai computer yana burgeni sosai,koh a lokacin da nake secondary na taba samu karramawa na musamman akan wanda yafi korewa a computer, atakaice dai Ni mutum ne mai son Tech.

Wasu kalubale ka fiskanta?

Kalubale da aka fiskanta suna da yawa, na daya akwai karanci abubuwan da zasu taimaka maka wajen karatu,ada wannan babban matsala ne da muka fuskanta, amma yanzu Alhmdllh wannan baya daga cikin matsala sakamakon komai ya wadata yanzu in kana da wayan ka da kuma intanet komai da kake bukata zaka iya samu a Google,amma ada hakan nada wahala sosai kamin ka san wani ma wanda yana harkan technology abu ne mai wahala amma yanzu Alhamdulillah a Anguwa zakaga mutum biyu uku suna harkan koma cikin abokai ba za’a rasa wanda suke harkan ba.

Rashin wutan lantarki shima wani kalubale ne,computer da ake aiki dasu a baya zaka samu duka computer ne da suna bukata wuta kuma basu rike chaji, in banda yanzu da ake samun computer masu rike chaji awa takwas awa goma ada zaiyu wuya ka samu computer mai rike chaji fiye da awa biyu kana aiki chaji zai kare kuma babu wuta dole ka tsaya da aikin da kakeyi.

Akwai kuma matsala intanet a lokacin bamuda hanyar samun intanet ba kaman yanzu da aka saba kowa na iya samun daman aiki da intanet, da ba haka abun yake ba ,ga kuma matsala mentorship ma’ana wanda yasan harkan da zai nuna maka yanda ya kamata kayi tareda baka shawara a da gaskiya akwai ƙaranci su sosai.

Wasu nasarori aka samu?

Alhmdllh cikin ikon Allah an samu nasarori masu yawa, na farko zuwan GDG community garin lafiya a 2014, wannan community ya taimaka sosai wajen bamu daman samun abubuwan koyan karatu kama daga bidio da sauran su wanda Google ke tura mana, bayan haka mun haɗu da mutane sosai masu hazaka wanda suka san harkan fasaha wannan ya taimaka sosai,har ya kai a yanzu muma muna iya yiwa wasu hanyar koyan wani fasaha koma samun aiki duk ta wannan dalilin sanin mutane da mukayi.

Usman tare da Jack

Bayan haka daga cikin nasarorin dana samu, na haɗu da Tsohon shugaba kamfanin Twitter Jack a 2019 duk saboda Community din har na jagoranci wasu mutane suma suka samu ganin shi Jack din ta sanadiya na duk wannan nasarori ne, kuma ta sanadiyar wannan harka na fasaha nayi tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje na samu daman haɗuwa da mutane masu yawa Alhamdulillah kwalliya ta biya kudin sabulu.

Shawara ga masu bukata shiga Harkan fasaha.

Shawara da zan bawa masu bukata shiga Harkan fasaha shine, na daya gaskiya sai mutum yayi hakuri ya jajirce, musamman in ya zama mutum ya shiga fannin ƙirƙirar(Programming) manhaja waya koh na yanar gizo dole sai yayi hakuri saboda kuskure daya zakayi wurin rubuta code naka sai kayi kusan kwana ɗaya biyu wani ma har uku ka kasa gane matsala din, wanna zai iya sawa mutum yaji ya hakura ma da abinda yake yi toh gaskiya dole sai da hakuri.

Shawara na biyu kuma shine mutum yayi kokarin shiga cikin jama’a da suke Harkan fasaha  musamman Community da ake dasu akwai damammaki sosai a community,ta wannan hanyar mutum zai samu sanin mutane masu yawa, kaga muma ta dalili community ne muka san su Jack da irin su Aniedi wanda daba don shigan mu community ba zaiyi wuya musan su gaskiya.yana da kyau mutum ya shiga cikin jama’a kar ka ware kanka gefe,cikin jama’a nan baka san waye zaka haɗu dashi ba wanda ta dalili shi zaka iya samun aiki koh ka haɗa wasu dashi.

Daga karshe abunda zance shine a shiga cikin jama’a kuma a taimakawa na baya wanda suke son shiga harkan tech kar mutum don ya samu ya shiga Harkan Tech kwalliya ta biya kuɗin sabulu ya rika yiwa na baya girman kai yana jiji dakai hakan bai dace ba,Shi a Harkan tech abunda muke farin ciki dashi shine ba’a boye ilimi, tunda mu haka muke ba kyashi ya kamata duk na bayan mu masu tasowa muyi kokari ganin suma sun tashi, atakaice zan tsaya anan a yanzu haka nine Nake kula da GDG keffi kuma nine nake kula da Twitter developer community na Lafiya baya ga sauran community da muke ciki Alhamdulillah Alhamdulillah Nagode.

Related Posts