Home » Bitmama sun kaddamar da Katin ATM na Crypto 

Bitmama sun kaddamar da Katin ATM na Crypto 

Kamfanin blockchain na Bitmama masu hada hadar kudin yanar gizo ma’ana crypto sun kaddamar da sabon tsari da zai bawa masu amfani da Bitmama daman mallakar katin ATM na zahiri wanda zasu turawa mutum a duk inda yake.

A sanarwa da suka fitar sunce sabon tsarin nasu zai bawa yan Afrika daman yin sayayya a kasashen waje ba tare da samun wani matsala ba na abunda zasu iya kashewa,kasantuwar a yanzu haka iya abunda zaka iya saya da katin ka na baki a waje kaidar baya wuce dala $100 wasu ma na shirin mayar dasshi dala $20.

Katin ATM na Bitmama zaka iya yin sayayya dashi har na dala dubu goma $10,000 duk wata ba tare da wani matsala ba,zaka iya amfani dashi a shafukan yanar gizo irinsu Bolt, Uber, Spotify, eBay,Facebook, da sauransu, ana iya amfani dashi kuma a ATM da POS wurin.

Zaku iya saka kudin yanar gizo irin USDT, USDC da cUSD kuma zaku iya kashe su kai tsaye ba tare da kun juya shi zuwa kudin zahiri ba, kawai kuna saka ATM naku zai juya yayi ba tareda bata lokaci ba.zaku iya sauke manhajan Bitmama a playstore da kuma AppStore.