Home » Tech Communities A Kasar Hausa

Tech Communities A Kasar Hausa

Tech Community wuri ne da yake hada mutane masu sha’awar fasaha, musamman ma fasaha Na’ura mai kwakwalwa,suna haduwa lokaci bayan lokaci domin karawa juna sani tareda koyan sabbin fasaha da kuma tattaunawa akan abinda ke tafiya a duniyar Fasaha.

Zaka samu wasu suna tattaunawa akan abunda ya shafi Fasaha Cigaban Yanar Gizo(Web Development) wasu Kuma sukan tattaunawa ne akan abunda ya shafi Yanda ake kirkirar manhajar Waya (Mobile Application) wasu kuma suna tattaunawa ne akan abunda ya shafi zane (Design).

Manyan kamfanonin da sukayi fice a harkan Fasaha a duniya suna taimakawa wurin samar da irin wannan yanayi da zai bawa masu sha’awar Fasaha samun daman hada kansu domin cigabansu a yankin da suke.

Kamfanin Google da kuma Facebook suna daya daga cikin kamfanonin dake wannan kokarin wajen ganin an samar da yanayin da zai bawa masu sha’awar Fasaha daman samun wurin da zasu na haduwa a duk lokacin da bukatan Hakan ya taso damin tattaunawa a tsakanin su da kuma taimakawa junansu wajen sanin sabbin fasaha da ake dasu.

Google sun samar da wani kungiya da ake kira GDG(Google Developer Group) inda masu sha’awar Fasaha musamman wanda ya shafi Fasaha da kamfanin na Google ke amfani dashi suke haduwa Lokaci bayan Lokaci damun koyan sabbin fasaha tareda tattaunawa akan duk wani sabon fasaha na Google dama wanda bana google din ba akwai kuma irin wannan da Google din suka sake samarwa domin dalibai yan makaranta gaba da secondary Wanda suke kiran shi da DSC(Developer Student Club)duk abu dayane da GDG bambancin kawai DSC ya takaita ne ga yan makaranta GDG kuma na kowa da kowa ne.

Facebook suma ba barsu a baya ba sun samar da nasu kungiyar wanda zai taimaka wajen hada masu sha’awar Fasaha domin haduwa su rika tattaunawa tareda karawa juna sani akan abunda ya shafi Fasaha, musamman fasaha da su kamfanin na Facebook suke amfani dasu suna kiran nasu da suna (Facebook Developer Circle).

Wadan nan dama sauran kamfanoni irin su da dama suna da irin wannan Groups din da daman gaske wanda suke taimakawa sosai wurin wayar dakai tareda samar da daman karatu ga masu sha’awar Koyan Fasaha,abun tambaya anan shine shin babu irin wannan kungiya ne anan yankin namu na arewacin Nigeriya koh kuma akwai su mune bamu san dasu ba?.

in Allah ya yarda zamu zo muku da amsohi wannan tamboyoyin a cigaban wannan rubutun namu ku cigaba da kasancewa da wannan shafin namu na TechHausa domin samun labarai dakuma Bayanai akan abunda ya shafi Fasaha cikin harshe Hausa.

Muna maraba da duk wanda zai bada gudumawa na rubutu Koh shawara akan abinda ya shafi Tech kimiya da fasaha cikin harshen Hausa zaku iya tura mana rubutu Koh shawara ta wannan adreshin na e-mail: munnir@techhausa.com

Related Posts