Home » TTLabs sunzo don taimakawa founders dake Arewa

TTLabs sunzo don taimakawa founders dake Arewa

Arewa an barmu a baya a bangarori daban daban na cigaba ciki harda abunda ya shafi kasuwanci da kana nan sana`a.Startup founders a Arewa na fiskanta matsaloli masu yawa kama daga ilimi da ake bukata don gudanar da Startup, shawara na yanda zasu tafiyar da harkokin su da kuma samun tallafi wajen cigabantar da kamfanin su.

TTLabs sunzo da tsari na musamman da zai taimaka wa founders na Arewa tun daga yanda zasu tsara Idea da suke dashi, za a taimka musu wajen shawari da kuma yanda zasu samar da MVP. za cigaba da basu taimako na yanda zasu shigar da abunda suke dashi kasuwa har su samu masu amfani da abunda suka kirkira.

Ba iya nan ba TTLabs zasu taimakawa founders wajen samun kudi daga masu saka hannun jari na ciki da wajen Nijeriya, wanda zasu zo su saka kudin su a startup domin habaka aiyukan startup din.

Suna kuma taimakawa founder ta hanyar samo mishi abokin gudanar da aiki Co-Founder, wanda zasu hadu suyi aiki tare don ganin idea da suke dashi ya samu karbuwa. Domin samun karin bayani da kuma sanin sauran abubuwan da TTLabs sukeyi zaku iya ziyartan su a shafin su na yanar gizo.

Related Posts