Home » Kamfanin Microsoft sun bude sabon Ofis A Legas 

Kamfanin Microsoft sun bude sabon Ofis A Legas 

Kamfanin microsoft sun bude katafaren ofishin su a legas karkashin shirin su na cigaban fasaha a Africa wanda suka kira da ADC, tun a shekarar 2019 ne suka fara gudanar da wannan shirin nasu inda suka dauki ma`aikata sama da Dari hudu aiki daga farawan su.

Suna kuma fatan daukan sabbin ma`aikata akalla mutum dari biyar  500 a wannan sabon ofisihin nasu,Gafar lawan manajan dake kula da wannan tsarina microsoft a Afrika shine ya bayyana hakan.

Ministan sadarwa Isa ali fantami shine ya jagoranci bude wannan sabon ofis din ya kuma yaba sosai da yanda kamfanin na microsoft suke kokari wajen kawo jigaba masu yawa a Afrika musamman ma a nan gida Nigeria, inda ya tabbatar da cewa a shirye gobnati take wajen bada hadin kai da kuma dukkan nin gudumawa da zaa bukata wajen ganin cigaban harkan fasaha a Nigeria.