Home » ESim sabuwar fasahar da zai maye gurbin Sim Card

ESim sabuwar fasahar da zai maye gurbin Sim Card

eSim sabon fasaha ne da zai bada daman mutum yayi aiki da wayan shi ba tareda ya saka Sim Card da muka saba amfani dashi ba,eSim yana zuwa ne a cikin waya tun daga kamfanin da aka buga wayan za’a saka esim din a cikin wayan(a injin wayan).

Abunda zakayi kawai bayan ka sayi wayan,sai kaje ofishin kamfanin Sadarwa da kake bukatan aiki dasu,su sai su saita maka wayan naka ta naura mai kwakwalwa su baka number shikenan.eSim zai iya daukan number fiye da daya akan shi zaka iya kana aiki da MTN, Glo da Airtel dukka number suna kan eSim naka.

Fasahan eSim ya dade ana amfani dashi a sauran kasashen duniya, a Nigeria makon daya gabata kamfanin MTN suka bada sanarwan fara aiki da wannan Fasaha,sun samu matsaya da hukuman NCC zasu fara gwajin eSim din na tsawon shekara daya.

Wayoyin da a yanzu haka suke da wannan Fasaha na eSim sune Google Pixel 3, Da kuma Pixel 4, sai kuman iPhone 11, 11 Pro, 11 Pro Max,iPhone XS, XS Max,iPhone XR,sai kuman wayoyin Samsung S20 Series, kamfanin Huawei, lenovo suma akwai wasu daga cikin sabbin wayoyin su da suke dauke da wannan Fasahan.

In kanada daya daga cikin wannan wayoyin sai ka garzaya ofishin MTN mafi kusa dakai domin a mayar maka number ka kan eSim naka.

Nan da shekara biyar dai sim card da muka saba aiki dasu a yanzu za’a neme su a rasa, dukkan wayoyi zasu fara fitowane da wannan fasahar na eSim