Home » MTN na Shirin kara farashin Data

MTN na Shirin kara farashin Data

Kamfanin MTN na shirin kara farashin Sayan Data a Nigeria da kuma kasar South Africa, sun bayyana hakan ne a wani rahoto da suka fitar na yanda aiyukan su ya kasance a farkon shekara zuwa yanzu.

A cikin rahoto sun nuna cewa yanayin matsin tattalin arziki da duniya ke fuskanta, suna ya shafi yanayin gudanar wa nasu, kuma hakan zai iya kaiwa ga kara kuɗin da suke chajin mutane Wajen sayan Data.

MTN sun saba fitar da irin wannan sanarwar dake nuna zasu kara kuɗin data kuma suna karawan koh a kwanakin baya sun kara Naira 50 akan wasu tsarin sayan data, inda daga baya kuma suka sake ragewa saboda korafi da suka ta samu daga abokan hulɗar su.

Related Posts