Home » Elun Musk ya zabi Linda Yaccarino mace ta farko a matsayin CEO Twitter

Elun Musk ya zabi Linda Yaccarino mace ta farko a matsayin CEO Twitter

Bayan kimanin watanni shida Elun na jagorancin Twitter, Elon Musk ya zabi tsohuwar shugabar tallace-tallace ta NBCUniversal, Linda Yaccarino a matsayin babban jami’in Twitter.

Ya bayyana haka ne Yau Jumma’a a shafin shi Na Twitter, inda yace Ya farin ciki gabatar da Linda a matsayin Shugabar kamfani na twitter. Inda yace zata maida hankali akan abinda ya shafi kasuwanci na Kamfanin, shi kuma zai maida hankali akan abinda ya shafi kirkira Sabbin fasaha a Twitter.

Ana ganin wannan a matsayin gyara na Farko da Elun yayi wanda ake sa rai zai sake farfaɗo da martaba Twitter, a yayin da Mutane da dama ke ganin kaman Elon ya lalata twitter da yanayi gudanarwa na kamfanin.

Related Posts