Home » MTN sun kaddamar da gwajin 5G a Nijeriya

MTN sun kaddamar da gwajin 5G a Nijeriya

Kamfanin sadarwa na MTN ya kaddamar da gwajin fasahar 5G a Najeriya, za’a fara gwajin me a birane bakwai, kamfanin MTN ya bayyana cewa an kafa hatsumuyoyin 5G guda 190 a fadin Najeriya musamman Legas da Abuja.
Wani rahoton BusinessDay yace an kaddamar da 5G a daidai ranar da hukumar sadarwa ta NCC tayi alkawarin za’a fara aiki da fasahan a Nijeriya.

Jihohin da aka fara da su sun hada da Lagos, Port Harcourt, Ibadan, Abuja, Maiduguri, Kano da Owerri.
Rahotanni sun kara da cewa nan da watan Oktoba, ana kyautata zaton MTN zai kafa hatsumiyoyi 500 zuwa 600 na 5G a fadin Najeriya.

Related Posts