Home » TALLA A STATUS NA WhatsApp

TALLA A STATUS NA WhatsApp

TALLA A STATUS

Manufar talla a ko’ina, ita ce, ta sadu ga mutane (da yawa). Shi ya sa ko a ‘Facebook Boost’ farashin tallar yana bambata da adadin ‘audience’ da Facebook zai sada tallar gare su, Misali:

• Mutane 489 – 1.4k = ₦3149.21 ne

• Mutane 1k – 2.9k = ₦6450.00 ne

• Mutane 8.3 – 24.1k = ₦50k ne

Ɗora talla a WHATSAPP STATUS na ɗaya daga cikin hanyoyin da ‘yan kasuwa ke tallata kayansu. Amma dai a riƙa taƙaitawa.

Kula! Ko ‘VIDEO’ ba a ɗora na sama da 30 seconds, ko ‘TEXT’ a status, ba ya wuce 700 characters (a, b, c…); duba da yanayin mutane.

Yana da kyau masu tallata kaya a Whatsapp Status su maida shi yadda mutane ke buƙata (kaɗan), saboda don mutane ake tallar. Kuma suna ƙorafi da yawa.

Ba dole sai kullum ka ɗora tallar duk (gaɓa ɗaya) kayan da kake siyarwa a Whatsapp Status ba, a’a; ka sa su daidai da yadda kowa zai iya buɗewa. Babu amfanin yin tallar da ba za a buɗe ba, ko za a samun ‘less audience’.

1. Kar ka ɗora tallar sama da shafi 5 (a ta yi yawa), mutane da yawa na ƙorafi, kuma kai ma don su kake ɗorawa, SAI KA YI YADDA SUKE SO ƊIN.

2. Idan kayan da kake son tallatawa na da yawa, ka yi amfani da PHOTO COLLAGE man (application mai haɗa hotuna wajen guda).

Idan a misali kana da niyyar ɗora shafi 20, za ka iya collaging hotuna huɗu-huɗu (waje guda) 4 x 5 = 20, shafi 20 ya koma 5.

Akwai apps na PHOTO COLLAGE (haɗa hotuna) a Playstore da AppStore:

Android

• Google Photos: bit.ly/3obeIWD

• PicCollage: https://bit.ly/3yJC36k

iPhone:

• Collage Maker apple.co/3aMjtCI

• PicCollage: Grid & Story Maker apple.co/3IMUzzs

3. Ko kuma ka maida tallar a koma periodic (lokaci-lokaci), misali,

• Daga ƙarfe 6 na safe zuwa 12 na rana, shafi 5.

• Daga ƙarfe 12 na rana, zuwa 6 na yamma, shafi 5.

• daga ƙarfe 6 na yamma, zuwa 12 na dare (ko wayewar gari), shafi 5

A rana ɗaya, ka yi talla ta shafin 15 kenan. Sai dai ko ka goge, mai amfani da ‘mods’ (GBWhatsapp, Whatsapp Plus, Whatsapp Gold, Clones, FMWhatsapp, OGWhatsapp, YO…) za su gani.

4. In dai kana kasuwanci, yana da kyau kana amfani da BUSINESS WHATSAPP, ingantacce ne daga asalin kamfani Meta. Akwai shi a Playstore da Appstore:

• Android: bit.ly/3AXc8Ld

• iPhone: apple.co/3ROgRov

WA Business yana da features a Business Tools:

• Ana ƙirƙirar ‘Business Profile’, ta yadda za ka iya sa address, profession, bayanin abubuwan da kake, email da website.

• Cataloging na kayan da kake siyarwa ko aiyukan da kake (za ka iya sa hoto 500 a WA Business Catalogue).

• Yana Auto-reply ga wanda ya ma chat, ko da kana OFFLINE (in ka saita).

• Za ka iya ‘LABEL’ na customers, misali, waɗanda su ka yi order/ba ka aiki, waɗanda ka yi wa delivery na kaya, waɗanda kake bi bashi, da sauransu.

• Za ka iya sharing ma customer wani ‘calagoue’. Misali, in ka raba catalogue’, na shaddodi, da yards, da atampa, da huluna… daban-daban, idan mutum na buƙatar shaddodi, sai ka masa sharing na ‘catalogue mai shaddodi, haka na sauran kayan.

Za ka iya amfani da WA Business da kuma normal Whatsapp a waya ɗaya. Whatsapp ya za ma personal, WA Business ya zama na kasuwanci.

5. Za ka iya buɗe GOOGLE BUSINESS PROFILE (google.com/intl/en_ng/business), nan ma za ka iya ƙirƙirar shafi, kana ɗora tallar kayanka, kamar website.

6. Ka ƙirƙiri shafi a LinkedIn.com, Jiji.com…, ka yi amfani da social media platforms don tallata kanka (skills) ko kayanka.

Aliyu M. Ahmad

20th Dhul-Hijjah, 1443AH

19th July, 2022CE

Related Posts