Home » Ayyukan da za ka iya yi daga gida a wannan shekara 2024

Ayyukan da za ka iya yi daga gida a wannan shekara 2024

TECH Hausa ta labarto cewa; ganin yadda ake samun sauye-sauye a yanayin gudanar da ayyuka a yau sakamakon bunkasar kimiyya da fasaha, sha’awar sassauƙa ayyuka, ingantacciyar rayuwa, da ci gaban fasaha. A cikin wannan sauyin, aiki daga gida ko a ce daga nesa shi ne mafi girma da ake iya samu a yau, sannan yana ba wa mutane damar yin watsi da zirga-zirgar yau da kullun da kuma yin sana’ar da kake da burin da sha’awar yi kai tsaye.

Shafin FlexJobs, amintaccen jagora ne idan aka zo batun gudanar da ayyuka daga gida, ya fitar da cikakken rahoto wanda ke bayyana fagagen aiki da ayyukan da ke rungumar wannan tsarin juyin juya halin na gudanar da aiki daga-kowane wuri kake. Tare da cikakkun bayanan dangane da neman aiki daga gida, wannan rahoton zai taimake ka ka kasance cikin shiri sosai a wannan ɓangare na gudanar da aiki daga nesa.

Ba duk fage ne suka rungumi wannan juyin juya halin gudanar da aiki daga nesa ba. Wasu masana’antu, duk da haka, sun fito a gaba-gaba, suna mai ba da dama ga waɗanda ke neman sassaucin gudanar da ayyukansu. Dubi waɗannan manyan ayyuka:

Kwamfuta Da IT: Daga sashen haɓaka manhaja (software) zuwa nazarin bayanai data analysis) zuwa kan inganta tsaron IT (Information Technology) da gudanar da cibiyar sadarwa, wannan sashen na fasaha tare da gudanar da aiki daga nesa suna da alaƙa sosai da sosai.

Huldar sha’anin kudi: Daga tattara lambobi zuwa sarrafa rahotannin kuɗi, ƙwararrun masu ƙididdigar kuɗi suna ƙara samun saurin shiga wajen gudanar da ayyukansu daga nesa.

Kasuwanci: ko ka kasance kwararre a ƙirƙira, ko a ƙwararre a fannin shafukan sada zumunta, duniyar kasuwanci tana ba da damarmaki da daman gaske kuma iri-iri wajen gudanar da ayyuka daga nesa domin ka buɗe ƙwarewarka ta ƙirƙira da nazari.

Kiwon lafiya: Baya ga fagen kula da mara lafiya kai tsaye, masana’antar kiwon lafiya tana da wasu bangarori da ake iya gudanar da ayyuka daga nesa a fannoni kamar rubutu kudaden magunguna, kwafin murya ko bidiyo zuwa rubutu, tare da gudanar da bincike.

Gudanar da Ayyuka: daga kiyaye manyan ayyuka zuwa daidaita su bisa tsari, ƙwararrun masu gudanar da ayyuka (Project Management) suna cikin wadanda ake da bukatuwa da su sosan gaske a cikin masana’antu daban-daban, kuma suna da damar yin aiki daga ko’ina.

Wadannan kadan ne daga cikin ayyukan da idan kuka kware a kansu za ku iya nema tare da gudanar da ayyukan daga nesa ba tare da kun je ofis ko ma’aikatar da ta dauke ku aiki ba.

Related Posts