Home » Hukumar NCC Ta Dakatar Da MTN Daga Hana Kiran Layukan Glo

Hukumar NCC Ta Dakatar Da MTN Daga Hana Kiran Layukan Glo

Hukumar Sadarwa ta Nijeriya, NCC ta bayar da umarni ga kamfanin sadarwa na MTN na Nijeriya da ya dakatar da shirinsa na katse layukan masu amfani da Globacom (Glo).

TECH HAUSA ta labarto cewa; a ranar 8 ga watan Janairu, 2024 NCC ta fitar da ankararwa na katse layukan Glo inda ta lamuncewa kamfanin MTN Nigerian Communications Plc., da ta fara yanke hulda da Globacom Limited (Glo) daga yau, 18 ga Janairun 2024 saboda doguwar takaddamar bashin haɗin gwiwa tsakanin bangarorin biyu.

NCC ta ce “A wajen bayar da amincewar, hukumar ta yi la’akari da illolin da hakan ka iya haifarwa ga masu amfani da layukan, a don haka ta ci gaba da shiga tsakanin bangarorin biyu domin su fito da hanyar sulhuntawa tare da kare muradun masu amfani da layukan da kuma tafiyar da harkokin sadarwa ta kasa,” in ji NCC. .

“Hukumar tana mai farin cikin sanar da cewa a yanzu bangarorin biyu sun cimma matsaya domin warware duk wata matsala da ke tsakanin su.

“A saboda haka, bisa karfin ikon da hukumar ke da shi a kan haka, Hukumar ta dakatar da yanke kiran layukan har na tsawon kwanaki 21 daga yau 17 ga Janairu, 2024.

“Duk da cewa Hukumar tana sa ran MTN da Glo za su warware duk wata matsala da ta kunno kai a cikin kwanaki 21, Hukumar tana jaddada cewa duk kamfanonin da ke gudanar da ayyukansu dole ne su warware basussukan haɗin gwiwa a matsayin wani abin da ya dace don bin ka’idojin doka na duk masu lasisi.

“Ya zama dole cewa masu gudanar da ayyukan sadarwa da sauran masu lasisi a cikin masana’antar sadarwa su kiyaye ka’idoji da sharuddan lasisin su, musamman kamar yadda yake kunshe a cikin yarjejeniyar haɗin gwiwa”, a wata sanarwa da hukumar ta sanyawa hannu, wanda Reuben Mouka, Daraktan yada labarai da hulda da jama’a ya karanta.

Related Posts