Home » Google Na Ci Gaba Da Korar Ma’aikata A 2024

Google Na Ci Gaba Da Korar Ma’aikata A 2024

Google ya kasance gaba-gaba wajen daukar ma’aikata a cikin ‘yan shekarun nan, amma ga dukkan alama yanayin ya soma yin juyin masa. A cikin wata sanarwa ga ma’aikata a ranar Laraba, Shugaban gudanarwa na Google, Sundar Pichai ya tabbatar da cewa za a ci gaba da korar ma’aikata a sassa da rassa da yawan gaske a kamfanin, inda kuma ya yi gargadin ci gaba da “kawar da masu taka muhimmiyar rawa” a cikin watanni masu zuwa.

Wannan ya biyo bayan dakatar da wasu ayyuka sama da 1,000 a sassa daban-daban a Google tun daga ranar 10 ga Janairu, a bangaren kayayyakin gudanar da ayyukan, tallace-tallacen kasuwanci, bincike, sayayya, taswirori, bangaren ayyukan injiniya, da kuma YouTube.

Hakanan ku tuna cewa a makon da ya gabata, Google ya sanar da cewa James Park da Eric Friedman, wadanda suka kafa Fitbit, sun tashi daga kamfanin. Bugu da ƙari, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin sake tsarawa, YouTube ya yanke shawara mai wahala wajen korar ma’aikata 100 a ranar Laraba.

Yayin da Pichai ya jaddada cewa wadannan raguwar ayyukan a Google ba su kai ma’auni na shekarar 2023 da aka rage ma’aikata 12,000 ba, ya yarda da cewa tasirin korar zai shafi ma’aikata da ƙungiyoyi. Ya dangana korar ma’aikatan da sabunta yanayin gudanar da wasu ayyukan tare da daidaita wasu ayyukan da kuma mayar da hankali kan gudanar da wasu ayyukan kan muhimman abubuwan da suka sa a gaba.

Wannan labarin na zuwa ne a cikin wani yanayi da masana’antar fasaha ta fada na daukar hayar ma’aikata da ma korar su daga aiki saboda rashin tabbas na tattalin arziki da karuwar gasa a tsakanin kamfanoni.

Kamfanoni kamar Amazon, Meta, da Twitter suma sun ba da sanarwar rage ma’aikata a cikin ‘yan watannin nan.

A yayin da Google yake ci gaba da kasancewa gidan fasaha mafi girma tare da bunkasa buƙatun masu amfani da shi, kamfanin a kwanan nan ya daukar matakai masu tsauri a 2024.

Ana fargabar Google zai ci gaba da rage ma’aikata a cikin shekarar nan da muke ciki.

Related Posts