Home » Jami’ar BAZE tare Da Hadin Guiwar Bankin Duniya Za Ta Koyar Da Ilimin Fasaha A Matakin Diploma Kyauta

Jami’ar BAZE tare Da Hadin Guiwar Bankin Duniya Za Ta Koyar Da Ilimin Fasaha A Matakin Diploma Kyauta

Jami’ar BAZE dake birnin tarayya Abuja tare da hadin guiwar bankin duniya ta fito da wani shirin karatu a matakin Difloma kyauta.

Jami’ar ta wallafa hakan ne a babban shafinta, inda ta samar da wani bangare da al’umma za su iya neman bukatar samun gurbin fara karatun.

Jami’ar ta ce za a gudanar da karatun ne a bangaren kwasa-kwasai har guda takwas da suka hada da: Artificial Intelligence, Blockchain Technology, Cybersecurity, Business Intelligence and Dashboard Creation & Development, Data Analytics, Digital Literacy, da kuma Software Engineering.

Sanarwar Jami’ar ta bayyana cewa; “Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta hannun Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta samu lamuni don samar da wani sabon shiri da Bankin Duniya ke tallafa wa mai suna: ‘Innovation Development and Effectiveness in the Acquisition of Skills (IDEAS) Project’ da nufin inganta tsarin TVET na kasar.

“Makasudin aikin IDEAS shi ne don haɓaka ƙwarewar samun ƙwararru a Nijeriya ta hanyar amfani da cikakkiyar hanya tare da magance muhimman abubuwan da ke cikin tsarin haɓaka fasaha. Zai bai wa masana’antu damar shiga cikin tsarin domin samun ‘yan ƙwadago da cunkoson albarkatu masu zaman kansu a cikin tsarin horo na yau da kullun”.

Jami’ar ta ce ga masu son samun damar gurbin karatun za su iya shiga shafinsu dake Intanet domin neman sanin cikakken bayani da hanyar da za su nemi wannan damar.

Related Posts