Home » Data Science Nigeria Ta Ziyarci Minista Bosun Tijani Akan Shirinta Na ‘Arewa Ladies4Tech’

Data Science Nigeria Ta Ziyarci Minista Bosun Tijani Akan Shirinta Na ‘Arewa Ladies4Tech’

Shugabancin ‘Data Science Nigeria (DSN)’ da kamfaninsa, DSNai, sun kai ziyarar ban girma ga mai girma ministan sadarwa, kirkire-kirkire, da tattalin arzikin zamani, Dr. Bosun Tijani, a ranar Juma’a 27 ga watan Oktoba 2023.

Ziyarar ya bai wa shugabannin DSN damar sanar da Ministan shirinsu na Arewa Ladies4Tech, wani shirin ba da tallafi ga mata a Arewacin Nijeriya wanda Google.org ke tallafawa tare da sanar da ma’aikatar game da irin karbuwar da suka samu a duniya a kwanan nan a bangaren ‘Artificial Intelligence (AI)’ a wata gasar duniya da Gidauniyar Bill da Melinda Gates ta shirya.

Har wala yau DSN ta tattauna batutuwan inda za su kulla alaka da ma’aikatar.

Ministan, Dakta Bosun Tijani, ya yi bayani dangane da shirin ma’aikatar wajen tallafawa da kuma ba da dama ga kamfanukan fasaha na gida, musamman a fannin AI / bayanai (data annotation).

Wannan yanki na AI yana ba da kyakkyawar dama ga ɗimbin guraben aikin yi ga masu farawa tare da ba da damar haɓaka ƙwarewar aikinka domin ci gaba da ayyuka.

Jagorancin DSN ya yi amfani da wannan damar wajen sanar da Ministan game da lambar yabo da karramawa ta duniya guda biyu da suka samu a kwanan nan a bangaren AI inda suka yi amfani da manyan nau’ikan harshe masu amfani da AI ta hanyar amfani da bayanan sauti da rubutu zuwa bidiyo a bangaren hada-hadar kuɗi da ilimi, bi da bi, wanda ya sami lambar yabo har guda biyu a wata babban gasar AI ta duniya, wanda Gidauniyar Bill da Melinda Gates suka shirya.

Wannan ya sanya kamfanukan guda biyu a cikin jerin mafi kwarewa guda 50 na duniya daga cikin sama da 1,300 da aka gabatar a duk faɗin duniya.

Bugu da kari, ministan ya yabawa shirin Arewa Ladies4Tech, shirin da aka samar domin mata zalla a Arewacin Nijeriya.

Ya sake jaddada aniyarsa ta kulla alaka da ma’aikatar wajen horar da matasa miliyan 3 nan da shekarar 2027, ta hanyar shirin 3MTT, wanda ke da nufin samar da kwararru a bangaren fasaha a fadin Nijeriya da kuma sanya kasar a matsayin mai fitar da masu hazaka.

Related Posts