Home » Hukumar Bai Wa Bayanan Ƙasa Tsaro, NDPC Ta Fitar Da Bayanan Kariya

Hukumar Bai Wa Bayanan Ƙasa Tsaro, NDPC Ta Fitar Da Bayanan Kariya

Hukumar kare bayanai ta Nijeriya (NDPC) ta kafa na’ura domin tabbatar da haƙƙin da yake akwai na bada kariya waɗanda suka shafi bayanai tare da bunƙasa yarda a ɓangaren tattalin arzikin dijital na Nijeriya.

A cikin wata sanarwa mai taken: ‘Guidance Notice on the Filing of Data Protection Compliance Audit Returns (CAR),’ Hukumar ta ba da shawarar masu kula da bayanai da masu sarrafa bayanai da su shigar da bayanan da suka dace ko kuma sun fuskanci haɗarin cire su daga cikin tsarin baya da kariyar Bayanai ta ƙasa (NaDPAP).

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ɗauke da sa hannun Babatunde Bamigboye, shugaban sashen shari’a, tabbatar da doka da oda na NDPC, ya ce masu kula da bayanai da sarrafa bayanan na ƙasa sun haɗa da bankuna, kamfanonin layin salula, asibitoci, makarantu, kamfanonin ICT, cibiyoyin bayanai da dai sauransu.

Idan dai ba a manta ba a kwanakin baya ne shugaban hukumar ta NDPC Dr Vincent Olatunji ya bayyana cewa hukumar na gudanar da taron horaswa kyauta ga jami’an da aka nada a bangaren kare bayanai na gwamnati da masu zaman kansu domin tabbatar da cewa Nijeriya za ta iya bayar da gudummawar da gogayya ga ci gaban tattalin arziƙin dijital na duniya.

Hukumar ta ƙara ba da shawarar cewa wakilai da ’yan kwangila da ke gudanar da sarrafa bayanai a madadin masu kula da bayanan ya kamata a horar da su kuma a shigar da su a tsarin Hukumar.

Related Posts