Home » Ƙalubale Biyar Da Kasuwancin Intanet Ke Fuskanta A Nahiyar Afrika

Ƙalubale Biyar Da Kasuwancin Intanet Ke Fuskanta A Nahiyar Afrika

TECH Hausa taabarto cewa; a yayin da ake yi wa nahiyar Afirika kallon tattalin arziƙinta na iya farfaɗowa musamman idan ta rungumi kasuwancin intanet da fasaha ta kawo, sai dai duk da rungumar wannan fannin da waɗansu suka yi, kafafen Intanet da suka shahara a ɓangaren hulɗar kasuwanci ake kuma hulɗa da su a nahiyar ba su da yawa.

Nahiyar Afirika ta kasance ɗaya daga cikin nahiyoyin duniya da suka rungumi fasahar kasuwanci ta shafukan intanet. Ana ganin masu sana’o’in dogaro na amfana da waɗannan hanyoyi wajen tallata hajojinsu tare da bunƙasa tattalin arziƙin nahiyar ta Afirika. Domin a ƙasashen da su ci gaba tuni wannan sabuwar tsari na kasuwancin Intanet ya yi zarra, domin tsarin wanda kimiyya da fasaha ya samar da shi, ɗimbin masu sana’o’in dogaro da kai ne suka yi masa ƙwamba domin ganin sun yi amfani da dabarbaru irin na kasuwanci wajen samun kwastamomi cikinsa domin su riƙa siyan hajarsu da suke tallatawa.

Hakazalika kamfanunnuka ma ba a barsu a baya ba wajen amfana da wannan tsari ta hanyar tallata hajarsu tare da samun ɗimbin riba mai gwaɓi.

Duk da irin ci gaba da sauƙi da wannan fasahar kasuwancin Intanet ke da shi, amma al’ummar Afirika suna da fuskantar gagarumin matsala da irin wannan kasuwanci. Domin har yanzu da yawan al’umma ba su iya bai wa wannan hanya muhimmancin da za su iya siyan kayan biyan buƙatarsu ta wurin ba. Amma ana ganin cewa idan har masu ruwa da tsaki akan harkokin kasuwanci a nahiyar Afirika suka bai wa wannan ɓangare muhimmanci, to za su fito da hanyoyin da za su iya magance matsalolin da ake fuskanta waɗanda ke sanya shakku da fargaba a zuƙatan mutane har suke nesantar hulɗar kasuwanci ta hanyar Intanet.

  1. Ƙalubale na farko shi ne akwai rashin yarda;

Mafi yawan mutanen Afirika har yanzu suna da tsoron siyan abu a shafin Intanet sakamakon samun labarurruka da ke nuni da yadda ake yin karo da masu zambo cikin aminci. Misali; waɗansu ba su da amincin su sanya bayanan abin da ya shafi asusun ajiyar bankinsu a shafin Intanet gudun ka da su faɗa hannun macuta. A yayin da masu ilimi kan sha’anin hulɗar kasuwancin Intanet suke gudun ka da ‘yan dandatse su wawushe musu kuɗi idan sun yi kutse a irin waɗannan shafin. Wannan dalilin da ma saura ya sanya ya zama dole masu kasuwancin Intanet su samarwa da shafukansu da suke hulɗar kasuwanci da su tsaro na musamman wanda zai bai wa mutum amincin hulɗa da su. Ko kuma su samar da hanyar nan ta mafi sauki ta sai an kawo min kayayyakin da na siya ta intanet har inda nake sannan na biya. Wannan zai yi magance wannan ƙalubale na farko.

  1. Tsadar Amfani da Intanet;

Wani ƙalubale na biyu kuma da ake fuskanta a nahiyar Afirika, shi ne tsadar amfani da shafukan Intanet. Ta yadda mutum ba zai iya amfani da shafukan Intanet ba sai ya siya abin da ake ce ma ‘DATA’ a turance, wanda za ka iya siyansa ko a ‘mega bytes’ ko ‘giga bytes.’ Sannan siyan wannan ‘DATA’ ɗin ba shi da sauƙi a nahiyar Afirika. Wannan yasa waɗansu suke ganin ba za su tsaya ɓatawa kansu lokaci suna shiga shafukan da ake siyar da kayayyakin biyan buƙatu a Intanet alhali duk za su iya samun su a shaguna garin su ko ma Unguwarsu. Wannan ya nuna ke nan, idan har ana son a magance wannan matsalar, wajibi ne gwamnati ta sanya hannunta a ciki wajen rage tsadar amfani da Intanet ɗin, ta hanyar tilastawa kamfanunnukan da suke da alhaki wajen samar da wannan ‘DATA’ ɗin, domin su rage kuɗin siyansu a baki ɗaya nahiyar Afirika.

  1. Yadda ake turo da kayan;

Matsala ta uku da yake shafar kasuwancin Intanet shi ne matsalar da ake fuskanta wajen turo wa da wanda ya siya kayan saƙonsa. Matsalar ƙarancin akwatun karɓar saƙonni da ake da su a Afirika yana ƙara dagula al’amarin kasuwancin Intanet. Inda ake samun waɗansu akwatun sam ba su aiki, waɗansu kuma suna aiki, amma ana fuskantar matsaloli da su. Shiyasa waɗansu shafukan kasuwancin Intanet ɗin sun fi maida hankali a kan amfani da motoci ko babura wajen aikowa da mutum kayansa, wanda wannan ke sanya kayan su ƙara tsada.

Domin magance wannan matsalar, ya zame wajibi waɗanda suke samar da shafukan hulɗar kasuwanci, su samar da hanya mafi sauƙi da za ta riƙa sauƙaƙawa wajen aikowa da karɓar waɗannan kayayyakin.

  1. Bambancin harshe da ƙabila;

Harshe na da matuƙar muhimmanci a kasuwancinmu na yau da kullum. Domin sai an fahimci abin da kake tallatawa sannan za a siya. Wannan ke nan yana ɗaya daga cikin ƙalubalen kasuwancin Intanet. Domin mafi yawan shafukan hulɗar kasuwancin Intanet, zaka same su cikin harshen turanci ake tallata hajar da ake son a siya. Kuma nahiyar Afirika nahiya ce da take da bambance-bambance harshe, da ƙabilu, sannan ga bambancin tsarin tafiyar da tattalin arziƙi da siyasa. Wannan yasa waɗansu shafukan kasuwanci na Intanet suke fuskantar matsaloli wajen aiko da kayyyakin da ake siya a wurinsu daga wata ƙasa zuwa wata ƙasa, domin sai sun biya musu haraji. Domin rage wannan matsalar yana da kyau, masu irin wannan kasuwancin, su samar da hanyar hulɗar kasuwanci da mutanen da suke yankinsu ne kawai, domin sauƙaƙawa da kuma rage fuskantar matsala.

  1. Rashin ilimi;

Ƙalubale na ƙarshe da ake fuskanta a hulɗar kasuwanci a nahiyar Afirika shi ne ƙarancin sani ko na ce rashin ilimin yadda ake hulɗar kasuwancin. Wannan ba ƙaramin cikas da matsala yake haifarwa ba. Domin da yawan mutane ba su san da zaman waɗansu shafukan Intanet ɗin za su shiga ba wajen yin wannan cinikayyar. Wannan ya nuna ke nan akwai aiki babba a gaban gwamnatoci a nahiyar Afirika, wajen ɓullo da hanyoyin da za a bai wa ɓangaren ilimi muhimmanci domin sake tsarkake al’ummar daga rashin sani zuwa al’umma masaniyya ta fuskoki daban-daban. Yin hakan, zai magance matsalar ƙarancin ilimi.

Related Posts