Home » Masu amfani da PalmPay sun kai mutum miliyan 30

Masu amfani da PalmPay sun kai mutum miliyan 30

PalmPay, mahajar hada-hadar kuɗi da aka kirkira ta hanyar fasaha, ya ce masu amfani da manhajar sun kara bunkasa zuwa mutum miliyan 30, inda kamfanoni miliyan 1.1 ke amfani da shi wanda ya haɗa da ‘yan kasuwa 600,000 da wakilai 500,000.

Manhajar ta hada-hadar kuɗin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis ya ce kamfanin ya kara samun hannun jari na har dala miliyan $140m.

Sanarwar ta ce “Tun lokacin da aka kaddamar da shi a Nijeriya a shekarar 2019 a karkashin lasisin gudanar da kudi ta wayar hannu, manhajar ya bunkasa zuwa masu amfani da shi har miliyan 30, kuma kamfanoni miliyan 1.1 da suka hada da ‘yan kasuwa 600,000 da wakilai 500,000 na mu’amala da shi,” in ji sanarwar.

Ana iya samun manhajar PalmPay akan Google Play Store da kuma iOS App Store a Nijeriya da Ghana.

PalmPay ya lashe lambobin yabo da dama a matsayin Cibiyar Kudi ta Shekara, da kuma lambar yabo kan mafi kyawun masu amfani da kafofin watsa labaru na zamani. Da kyautar Manajan shekara wanda aka bai wa manajan kasuwanci na manhajar wato Kevin Olumese.

Related Posts