Home » Hanyoyin Ribatar Shafukan Sada Zumunta Cikin Sauƙi A Ƙarni Na 21

Hanyoyin Ribatar Shafukan Sada Zumunta Cikin Sauƙi A Ƙarni Na 21

Kimiyya abu ne mai muhimmanci a rayuwar da kullum. Domin tana ba da gudummawa sosai wajen sauƙaƙa waɗansu lamarun rayuwar, duk da matsalolin da yake haifarwa, amma bana tunanin a yau duniyar za ta iya tafiya yadda ya kamata ba tare da ilimin kimiyya da fasaha ba.

A yau duniya na ci gaba da haɓaqa da bunƙasa a wuri guda, ta yadda a yanzu daga ɗakinka zaka iya hulɗa da ɗimbin al’umma a sassa daban-daban na duniya wanda kimiyya da fasaha ya kawo hakan. Sannan kuma ba komai ya ja za hakan ba illa yadda ɗan Adam ɗin dake rayuwa a cikin duniyarnan ke bunƙasa tunaninsa wajen sauƙaƙawa rayuwarsa ta yau da kullum. Waɗannan dalilai dama sauran masu tarin yawa ya ja za al’umma daban-daban a sassa daban-daban suke bunƙasa tunaninnukansu wajen samar da abin da al’umma za ta amfana baki ɗaya. Su ma waɗanda suka samar da abin su amfana da shi ta janibobi daban-daban.

Daga cikin wannan fasahar da al’umma ta samar kuwa, akwai shafukan sada zumunta, inda a yau waɗannan shafuka suka taka muhimmiyar rawa wajen ilmantarwa, nishaɗantarwa, faɗakarwa, wa’azantarwa, tare da gurɓata ma tarbiyya a lokaci guda. Sannan a yau irin waɗannan shafukan sada zumunta da ake da su kamar Facebook, Twitter, Instagram, YouTube, WhatsApp da sauran su, ya ja za waɗansu gurɓatattu na amfani da shafukan wajen cimma manufarsu ta siyasa ko ta ƙabila ko kuma ta neman lalata tarbiyyar al’umma. Sannan waɗansu a yau suna amfani da irin waɗannan shafuka wajen rura wutar rikici da gaba a tsakanin al’umma daban-daban.

Ba ya ga haka ma, ba a nan kawai ba, har wala yau waɗansu na amfani da irin waɗannan shafukan wajen qirqirar labarun qarya domin yaɗa su cikin al’umma da nufin haddasa rikici ko husuma, waɗansu kuma da nufin nishaɗi, yayin da waɗansu kuma da wata ɓoyayyiyar manufa da suke son cimmawa. Irin wannan lamari babban barazana ne, kuma haɗari ne ga ma zaman lafiyar al’ummar da suke da irin waɗannan ɗabi’ar. Ina ga ma wannan yana daga cikin dalilai da suka sanya gwamnatin tarayya ta tashi haiƙan wajen ganin ta yaƙi masu irin waɗannan ɗabi’a na yaɗa labarun ƙarya da na boge da kuma na kalaman ɓatanci.

Duk da dai waɗansu na ganin ƙudurin na gwamnatin tarayya akwai alamar tambaya, musamman idan aka yi la’akari da irin siyasar ƙasar, amma da a ce gwamnatin tarayya za ta yi gaskiya a yaƙin da za ta yi da kalaman ɓatanci, ƙarya da na boge, to da tabbas kowanne ɗan ƙasa abin ya yi lale marhaban da wannan mataki da gwamnatin tarayya ke son ƙaddamarwa. Amma duk da irin waɗannan kule dake cikin waɗannan shafukan na sada zumunta, hakan ba zai hana a matsayin mutum a ƙashin kansa ya ribaci shafukan ba wajen ci gabantar da rayuwarsa da ta al’ummarsa ma baki ɗaya ba.

A yau muna ganin yadda matasa da masu shakaru daban-daban suke amfani da waxannan shafukan wajen gudanar da ayyukan alheri wanda ke shafar vangarorin al’umma daban-daban, tun kama daga marasa lafiya, xalibai, waxanda suka samu haxari, ‘yan gudun hijira, masu buqatar taimakon gaggawa, mata masu al’ada da dai sauran su.

A taqaice, wannan ya nuna ke nan, akwai buqatar masu amfani da irin waxannan shafukan su jajirce wajen ganin ba kawai sun vata lokutansu wajen yin hirarraki waxanda ba za su amfane su ba da komai, akwai buqatar su ribaci waxannan shafukan ta hanyar yaxawa ko tallata wani abu da zai amfane su a qashin kan su, da kuma al’ummarsu baki xaya.

Misali; a yau idan kai xan kasuwa ne, zaka iya amfani da waxannan shafukan wajen tallata hajar da kake siyarwa, kuma tabbas za ka samu waxanda za su nemi inda kake kuma su zo su siya. Waxansu qila a garin da kake suke, amma ba su san kana yin sana’arnan ba, amma sakamakon tallata sana’ar da za ka yi a shafinka da ke irin waxannan shafukan sada zumuntan, sai ka ga wani ya fahimci ashe wuri guda kuke rayuwa, sai ya neme ka, ka ga kuma ya siya daga gare ka. Ba ya ga haka ma, waxansu waxanda ba kusa suke da kai ba, za su iya neman cewa za su siya abin da kake siyarwa, kuma a qarshe za ku tattauna da su yadda za ku aika musu da kayyyakin da kuke siyarwa har inda suke. Idan mutum ya yi hakan, da mai ya yi asara? Ka ga amfanuwa ya yi, kuma ya ribaci shafin wajen bunqasa kasuwancinsa, wanda hakan zai taimake shi ta hanyoyi daban-daban. Sannna idan har al’umma ta fahimci cewa ga sana’ar sa kake yi, za ka yi mamakin yadda za a riqa nema daga gare ka domin an siya.

Haka zalika idan mutum shi Malami ne, zai iya shirya wani ilimi na musamman na daban da kake ganin ya voyu ga al’ummar da kake tare da su a shafukan sada zumunta, ka buxe wani zaure a shafin, ka riqa karantar da waxanda suke da buqata a kyauta, idan har waxanda kake yi domin su suka fahimci muhimmancin abin da kake karantar da su, wata rana ko kuxi ka sanya musu su biya ka kafin ka ilmantar da su, ina mai tabbatar maka cewa za su biya domin amfana daga iliminka.

Hakazalika, masu makaranta su kan su za su iya amfani da waxannan shafukan wajen tallata makarantarsu da abin da makarantar ta qunsa da kuma me suke yi, ta hanyar amfani da salo na gaskiya ba na yaudara ba wajen ganin al’umma ta karvi abin hannu bibbiyu, idan ka yi hakan, shin ba a ribaci waxannan shafukan ba?

Haka zalika, masu ayyukan taimakon gaggawa, ba da agaji, qungiyoyi taimakon al’umma, masu bai wa asibitoci gudummawar jininsu domin ceton rai, da kuma masu kai xauki a duk lokacin da buqatar hakan ta ta so, masu taimakon marasa lafiya, da dai sauran su, suma za su iya amfani da waxannan shafukan wajen tallata ayyukansu, yin hakan yana qarfafa waxanda suke kwance suke ganin kamar ba wajibi bane su taimaki al’ummarsu. Hakan kuma na qarfafa waxanda suke ganin kamar komai ya xoru ne akan gwamnati kawai. Idan har za a samu ximbin al’umma wanda za su riqa irin waxannan taimakon na yau da kullum, to tabbas za a samu waxansu sauye-sauye a waxansu lamarun da ke tafiya a qasarnan.

Alal misali ma, ko da a ce kwashe kwatar Unguwarku kuka yi, ko share ta, ko xaukar hotuna ku sanya a waxannan shafukan sada zumuntar, hakan na iya qarfafa wani ba ka sani, ta yadda suma za su kawwana kan su a xaixaiku ko a qungiyance, sai ka ga suma sun je sun yi share Unguwarsu tare da kwashe dukkanin Kwalbatin da ta cunkushe musu.

Ba don na qarqare ba, zan taqaita a nan sai kuma wani makon mai zuwa sai mu tattauna wani lamarin na daban. Amma hanyoyin ribatar shafukan sada zumunta a yau, suna da yawan gaske, wanda za a iya rubuta littattafai masu tarin yawa.

Related Posts