Home » Gwamnatin Gombe Da NITDA Sun Kulla Yarjejeniyar Horas Da Matasa Da Mata Ilimin Fasaha

Gwamnatin Gombe Da NITDA Sun Kulla Yarjejeniyar Horas Da Matasa Da Mata Ilimin Fasaha

A wani gagarumin ci gaba domin ci gaban fasaha da gudanar da mulki a Nijeriya, Kashifu Inuwa, Darakta-Janar na Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA), ya bai wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe tabbacin karfafa hadin gwiwa a wasu bangarorin wajen horas da ilimin fasaha.

Tabbacin ya zo ne a ziyarar da Gwamnan ya kai hedikwatar NITDA da ke Abuja, inda shugabannin biyu suka tattauna kan fadada dangantakar da ke tsakanin NITDA da jihar Gombe.

Tattaunawar ta ta’allaka ne kan yadda za a haɓaka shirye-shiryen ilmantar da matasa ilimin dijital tare da ƙarfafa ayyukan gudanar da mulki ta yanar gizo a cikin jihar, tare da manufar bunkasa ingantaccen tsarin gudanarwa wajen biyan bukatun ‘yan ƙasa.

Inuwa ya bayyana kudurin NITDA na tallafa wa kyawawan manufofin jihar Gombe wajen sarrafa dukkan ayyukan gwamnati a jihar, yana mai jaddada himmar hukumar wajen samar da kwararrun fasaha, kayan aiki, da jagoranci don tabbatar da hadewar fasahohin zamani a sassa daban-daban na jihar.

Tattaunawar ta yi la’akari da wasu fannoni na musamman domin inganta iya aiki, samar da ilimin fasaha tare da tsare-tsare don kara kaimi wajen kafa hukumar IT ta jiha da za ta samarwa matasa da matan Gombe sana’o’in hannu na zamani ta hanyar samun ingantaccen horaswa.

Related Posts