Home » Shirin NIGCOMSAT Na Amfani Da Tsarin Karatu Na Zamani Zai Sauya Fasalin Ilimi a Nijeriya

Shirin NIGCOMSAT Na Amfani Da Tsarin Karatu Na Zamani Zai Sauya Fasalin Ilimi a Nijeriya

Manajar Darakta kuma Babbar Jami’ar Kamfanin Sadarwar Tauraron Dan Adam (NIGCOMSAT), Misis Nkechi Egerton-Idehen ta bayyana shirin kawo sauyi ga ilimi a Nijeriya ta hanyar raba tsarin fasalin ilimi na zamani na Cibiyar ta NIGCOMSAT bda ta kira da ‘NIGCOMSAT’s Educational Technology (EdTech)’.

An bayyana hakan ne a yayin taron masu ruwa da tsaki na NIGCOMSAT da aka gudanar a Abuja.

Egerton-Idehen ta bayyana cewa, tsarin koyon karatu na EdTech, ta hanyar amfani da hanyoyin sadarwa na tauraron dan adam, na da nufin kawo gagarumin sauyi a fannin ilimi a Nijeriya. Ta yi tsokaci kan kalubalen da makarantu ke fuskanta, inda ta yi nuni da cewa, a yayin da ake kokarin shigar da fasaha cikin ilimi ta hanyar samar da dakunan gwaji na ICT da na’ura mai kwakwalwa, amma rashin samun saukin hanyoyin sadarwa na intanet ya kasance babban abin da yake kawo cikas ga cimma wannan manufa.

Ta jaddada cewa yawancin cibiyoyin ICT ba a iya amfani da su ba yadda ya dace saboda rashin kyakkyawan karfin intanet, a yayin da ta ce wasu kuma ana amfani da su ne kawai wajen koyar da ilimin kwamfuta a maimakon fadada bincike na samun cikakken damar koyo.

Manajan Daraktar ta ce yana da fatan cewa sauyawa zuwa amfani da intanet na tauraron dan adam zai haɓaka haɗin gwiwa da ƙarfafawa a cikin azuzuwa, haɓaka tunani mai muhimmanci da warware matsaloli, da sauƙaƙe gudanarwa, takaddun bayanai, da isar da abubuwan ilimi cikin sauki.

Domin tallafawa ci gaba a fannin ilimi, Egerton-Idehen ta zayyana muhimman fannoni guda uku da za a fi mayar da hankali: haɓaka ƙirga da karatu a makarantun firamare, kafa dakunan karatu na dijital domin makarantun sakandare, da ƙarfafa ƙirƙirar abubuwan karatu ga malamai a yayin aiwatar da tsarin sarrafa koyo.

Bugu da ƙari, Manajan Daraktar ta gabatar da ƙwarewar da abokan huldarta ke da shi a bangaren sadarwa da fasaha.

Related Posts