Home » Bayan Sakin GPT-4 Fiye Da Mutum Miliyan 100 Ke Amfani Da OpenAI ChatGPT A Duk Mako

Bayan Sakin GPT-4 Fiye Da Mutum Miliyan 100 Ke Amfani Da OpenAI ChatGPT A Duk Mako

A taron farko na masu haɓaka manhajar OpenAI, Shugaba Sam Altman ya bayyana cewa ChatGPT, sanannen AI chatbot, masu amfani da shi a duk mako sun kai miliyan 100. Sannan ya kuma gabatar da sabon samfurin manhajar da suka kira da GPT-4 Turbo, wanda yake da ƙarfin gaske fiye da ChatGPT.

Sai dai ya ce sabon samfurin manhajar ta AI da mai samar da rubutu da aka bunƙasa tana da tsadar gudanarwa.

ChatGPT, wanda aka saki shekara guda ke nan da ta gabata, ya samu karɓuwa sosai cikin sauri, inda ya tara kimanin masu amfani da shi miliyan 100 a kowanne wata a cikin watanni biyu na farko.

Altman ya bayyana cewa sama da mutum miliyan biyu da suke masana ne a ɓangaren samar da manhaja a yanzu suke amfani da dandamalin, inda ya ce kashi 92% na kamfanoni 500 da suka shahara ne ke amfani da shi.

Ɗaya daga cikin muhimman sanarwar da aka yi a taron shi ne gabatar da GPT-4 Turbo, samfurin AI na zamani da aka haɓaka shi wanda aka gina shi ta hanyar ɗaga darajarsa zuwa 128k, wanda hakan zai ba shi damar fahimtar daidai tare da bayar da amsa na fiye da shafuka 300 na rubutu a cikin hanzari a kuma lokaci ɗaya idan ka tambaye shi.

Wannan sabon samfurin na AI ba kawai ƙarfinta da kaifi basirarta bane kawai abin kallo, tana da tsada da wajen amfani da ita.

Related Posts