Home » Akwai Damarmaki A Nijeriya, Sakon Shugaban NITDA Ga Masu Saka Hannun Jari Na Kasashen Duniya

Akwai Damarmaki A Nijeriya, Sakon Shugaban NITDA Ga Masu Saka Hannun Jari Na Kasashen Duniya

A wani yunkuri na sanya Nijeriya ta zama fitacciya kuma gawurtarciya a kasuwannin zamani na duniya, Babban Daraktan hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa (NITDA), Inuwa Abdullahi ya yi kira ga masu zuba hannun jari a duniya da su yi la’akari da yadda kasar ke bunkasa.

Ya jaddada hakan ne a yayin ziyarar ban girma da tawagar Seidor, karkashin jagorancin jakadan kasar Sipaniya a Nijeriya, Juan Seli, suka kai hedikwatar kamfanin na NITDA.

Dakta Usman Abdullahi Gambo wanda ya wakilci shugaban na NITDA, kuma Daraktan kula da hanyoyin samar da ababen more rayuwa na zamani (ITIS), ya bayyana muhimmancin dake cikin wannan ziyarar, inda ya jaddada dimbin damammakin da yake akwai a cikin kulla alaka.

Da yake ba da haske kan bangaren da za su kulla alaka wanda ya hada da sarrafa basira, sabbin abubuwa, abubuwan gida, da haɓaka iya aiki, Babban Daraktan ya bayyana ayyukan da NITDA ke ci gaba da yi, a madadin sauran hukumomin gwamnati. Musamman ma, an samar da Cibiyar AI da mutum-mutumi (Robotics) ta kasa (NCAIR) a matsayin wani muhimmin shiri na samar da yanayin da zai dace wajen ganowa da kuma amfani da sabbin dabaru ga matasan Nijeriya domin ci gaban kasa.

“A cikin fahimtar manufofin cibiyar, yawancin matasa suna fuskantar kalubale akai-akai domin gwada basirarsu domin samar da mafita da za su magance kalubale a duk sassan tattalin arziki, magance matsalolin gaggawa da na nan gaba tare da illar da yake haifarwa ga duniya,” in ji Abdullahi.

Babban Daraktan ya kuma yi tsokaci kan shirin 3MTT, wani shiri da ma’aikatar sadarwa, kirkire-kirkire da tattalin arziki na zamani ta gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da niyyar gina ‘yan Nijeriya miliyan uku. Wannan shirin ya yi daidai da hangen nesa na samar da guraben aikin yi na zamani miliyan biyu nan da shekarar 2025, kamar yadda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tsara.

Da yake ba da tabbacin ga Seidor ya ce NITDA a shirye take domin zurfafa tattaunawa don yin hadin gwiwa, Abdullahi ya bayyana kyakkyawan fata game da fa’idojin da za a iya samu daga hadin gwiwar. Ya jaddada kudurin hukumar na samar da sabbin fasahohi da mafita na dijital.

Related Posts