Home » Ku san sabuwar shugabar Kamfanin Sadarwar Tauraron Dan Adam Ta Nijeriya, NIGCOMSAT

Ku san sabuwar shugabar Kamfanin Sadarwar Tauraron Dan Adam Ta Nijeriya, NIGCOMSAT

A ranar Laraba, 11 ga Oktoba, 2023, Shugaba Bola Ahmed Tinubu (GCFR) ya nada Misis Nkechi Jane Egerton-Idehen a matsayin Manajan Darakta kuma Babbar Jami’ar Kamfanin Sadarwar Tauraron Dan Adam wato NIGCOMSAT.

Nkechi Jane Egerton-Idehen Babbar Jami’ar Fasaha ce, Marubuciya kuma mai saka hannun jari ce. Ita ce Shugabar Kasuwanci ta Gabas ta Tsakiya da Afirka na kamfanin Meta (Facebook). Kafin nan, ta kasance Manajar gudanarwa ta kasa mai kula da Nijeriya, kuma Daraktar Tallace-tallacen Yanki na reshen Afirka ta Yamma a kamfanin Avanti Communications Group PLC, kamfanin sadarwa na Birtaniya tare dake da tarin tauraron dan adam a sararin samaniya. Ta yi aiki a wurare daban-daban tun kama daga mai bada shawara, gudanar da ayyuka, lura da kasuwanci, a babban kamfanin kayayyakin sadarwa ta Ericsson. Ta kuma yi aiki a matsayin jagora a kamfanin Nokia Siemens Network a Yammacin Afirka.

An haifi Misis Egerton-Idehen kuma ta girma a birnin Legas na Nijeriya. Ta kammala karatun digiri na biyu a fannin injiniyan lantarki a shekarar 2001 a Jami’ar Nijeriya, dake Nsukka. Ta ci gaba da karatunta a Makarantar Kasuwanci ta Warwick da ke Birtaniya, inda ta sami digiri na biyu. Ta kuma sami ilimin gudanarwa a Makarantar Kasuwancin ta Harvard da Makarantar Gudanarwa ta Yale a Amurka.

Ta yi aiki a bangaren sadarwa a Afirka sama da shekaru 17. Iliminta na fasaha, da kuma gogayyar da take da shi na sarrafa sarkakiyar da yake akwai na kulla alaƙa tsakanin masu ruwa da tsaki, tare da nuna ƙwarewa wajen sarrafa ƙungiyoyi da ƙirƙirar dabarun tallafawa da bunkasa kasuwanci wadanda ake ganin sune mabuɗin nasararta.

Kasancewarta ɗaya daga cikin mata da ke jagorantar manyan wuraren kasuwanci a masana’antar fasaha ya sanya Jane ta samu ƙwararewa tare da fuskantar ƙalubale.

Tattaunawa da takwarorinta mata masu gudanarwa a duniya, ta shirya wani taro a Ericsson inda ƙwararrun shugabannin mata masu tasowa za su iya tallafawa juna wajen haɓaka sana’o’insu. Gagarumin nasarar da dandalin ya samu ya sa ta samar da Dandalin Women and Career, domin kai wa ga mata dake wajen kungiyarta tare da tallafa wa mata masu neman sana’o’i bayan sun kammala karatu.

A cikin Maris 2020, ta buga littafi mai sun ‘Be Fearless: Give Yourself Permission To Be You’. Littafin ya samo asali ne daga gogewar data samu na fiye da shekaru 15 a matsayin mai gudanarwa a bangaen sadarwa a Afirka, domin taimakawa mata don gina sana’a mai dorewa, musamman a masana’antar STEM da maza suka mamaye. Littafin ya shiga jerin manyan littafai bakwai da aka fi saya a Amazon a ranar 17 ga Maris, 2020, ina ya hau har zuwa mataki na ɗaya a cikin Rukunin Da’a na Kasuwanci da Ilimi.

Related Posts