Home » Paystack ya samu izinin gudanar da ayyukansa a kasashen Masar, Rwanda, da Cote d’Ivoire

Paystack ya samu izinin gudanar da ayyukansa a kasashen Masar, Rwanda, da Cote d’Ivoire

Kamfanin ayyukan kuɗi na Nijeriya, Paystack, ya sami lasisin fara ayyukansa kasashen Masar da Rwanda.

Har ila yau rahotanni sun nuna cewa ta yi haɗin gwiwa da manyan cibiyoyin kuɗi domin ba da ayyukansu na kuɗi a kasar Cote d’Ivoire.

Paystack ta bayyana hakan ne a shafinta na yanar gizo, wanda hakan ke nuni da cewa a hukumance, kamfanin ya fadada ayyukansa zuwa wadannan kasashe uku, wanda ya kawo adadin kasuwannin da yake aiki zuwa bakwai da ya hada da Ghana, Kenya, Nijeriya, Afrika ta Kudu, Cote d’Ivoire, Masar, da Rwanda.

Paystack ya ce zai fara fadada ayyukansa ne zuwa cikin waɗannan ƙasashen a mataki na biyu mai zaman kansa wanda zai taimaka masa “wajen ɓunkasa kamfaninmu a cikin kowanne ɗayan waɗannan ƙasashe, aiwatar da hanyar samun ra’ayi, da kuma tabbatar da cewa mun gina kafa cikin sauri, wacce za ta zama abin dogaro, tare da nuna ƙwarewa wajen biyan kuɗi ga kowanne kasuwanci.”

Related Posts