Home » NITDA Ta Bude Dama Ta Musamman Ga Mata Masu Sha’awar Harkar Fasaha

NITDA Ta Bude Dama Ta Musamman Ga Mata Masu Sha’awar Harkar Fasaha

Shin ke mace ce da ta kafa kamfani a bangaren fasaha, kowacce take son bunkasa bangaren fasaha, ko mai sha’awar fasaha? Wannan dama ce gare ku domin cimma wannan manufa domin makomar fasaha a Nijeriya. Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa, NITDA ta hanyar ofishin reshenta na ‘Nigerian Digital Innovation (ONDI)’, tana gayyatar ku da ku kasance cikin wannan dama ta musamman mai abin mamaki wanda shi ne shirin horas da mata da aka kira da ‘Female Founders TRAINING programme’.

Wannan yunƙuri na da nufin tallafawa tare da ƙarfafa mata a Nijeriya domin yin amfani da fasahar dijital don gina ingantacciyar sana’a.

An sadaukar da shirin horon ne domin ganowa da kuma bayyana sabbin dabaru da kirkire-kirkire na tushen fasaha da siddabaru da hanyoyin wanda mata za su kirkiro a Nijeriya.

Manufar ita ce a daidaita bambance-bambancen jinsi a cikin masana’antar fasaha da kuma karfafa samar da damar yin aiki na dijital ga mata.

Ranar ƙarshe ta rufe wannan dama: 7 ga Nuwamba, 2023.

Related Posts