Home » Bankin Fidelity Ya Maido Da Tura Kudi Zuwa Moniepoint, Palmpay, Opay Da Sauransu

Bankin Fidelity Ya Maido Da Tura Kudi Zuwa Moniepoint, Palmpay, Opay Da Sauransu

Bankin Fidelity PLC, a ranar Juma’a, ya mayar da batun ci gaba da tura kudi zuwa asusun Moniepoint, PalmPay, OPay da Kuda Bank.

Bankin na Fidelity ya cire bankunan ne daga jerin wadanda za a iya turawa kudi ta hanyar bankin na su saboda karuwar zamba da kuma rashin tabbaci kan kwastomomin da ke amfani da bankunan.

TECH Hausa ta ruwaito cewa a yanzu bankin ya dawo kuma za a iya tura kudade zuwa ga bankunan da ta dakatar bayan da hukumar dake kula da harkokin banki na Nijeriya (NIBSS), ta nuna rashin jin dadinta da matakin da bankin Fidelity ya dauka na toshe rashin tura kudaden zuwa wadannan bankuna.

Mista Bemigho Awala, Manajan yada labarai da hulda da jama’a na Moniepoint Inc., shi ne ya tabbatar wa da majiyarmu cewa an magance lamarin.

Ya kara da cewa bankin na Moniepoint Microfinance Bank “yana gudanar da kasuwancinsa ne cikin bin ka’ida da kuma kiyaye manyan dokoki da ka’idojin da Babban Bankin Nijeriya ya fitar kan al’amuran da suka shafi ka’idoji da dokoki na sanin wane ne kwastomanka wanda aka fi sani da ‘Know Your Customer’ (KYC)’.

“A gare mu, KYC ta zama ginshiƙi wajen amana, tabbatar da tsaro, da kuma bin ƙa’idodin na hulda. KYC ba takaitawa ba ne kawai; yana wakiltar wani muhimmin tsari na matakai da aka tsara domin tabbatarwa da kuma tabbatar da ainihin abokan cinikin da ke yin mu’amalar kuɗi”.

Wata majiya a PalmPay ta tabbatar da faruwar lamarin tana mai cewa Bankin Fidelity yanzu ya koma matsayin da ya ke a da. “Wannan lamari ne da aka kammala yayin da abokan ciniki ke yin mu’amala a kan dandalin Bankin Fidelity ba tare da an sake hana wa ba”, in ji majiyar.

Babban makasudin KYC shi ne hana cibiyoyin kuɗi shiga cikin ayyukan haram kamar satar kuɗi, ba da tallafi ga ‘yan ta’adda, da zamba.

Related Posts