Home » Jumia Ta Bude Wani Tsari Da ‘Yan Kasuwa Za Su Bunkasa Kasuwancinsu A Nijeriya

Jumia Ta Bude Wani Tsari Da ‘Yan Kasuwa Za Su Bunkasa Kasuwancinsu A Nijeriya

Sashen tallace-tallace ta Jumia da aka fi sani da ‘Jumia Advertising’ a turance, ya kaddamar da wani tsari da ya kira da ‘Programmatic Advertising service’, domin bai wa ‘yan kasuwa da kamfanuka wata dama domin su bunkasa kasuwancinsu a Nijeriya.

An tsara shirin ne domin ƙarfafa masu siyarwa da masu tallace-tallace tare da wata fasaha mai muhimmanci da dabarun sarrafa bayanai, shirye-shiryen tallace-tallacen wanda zai buɗe sabbin hanyoyin haɗin gwiwa da haɓaka tsarin gudanar da kamfe bisa fasahar zamani da ke haɓaka cikin sauri take kuma juya yanayi talla a zamance.

Jumia na da mutum sama da miliyan 27 wadanda suke bibiyar shafinsu a kowanne wata daga ƙasashen Afirka da dama. Talla a Jumia yana bada wata babbar dama ga kanana da matsakaitan kamfanoni domin isa ga ƙarin masu siyayya da yawan gaske ta Intanet.

Shirin tallace-tallace na Jumia, yana bai wa masu talla damar riskar masu bukatar irin abin da suke siyarwa, kasafin kudinsu, tare da haɓaka ayyukan kamfen ɗin su ta hanyar mashigarsu na ainihi a shafin na Jumia.

Za su iya yin amfani da zaɓuɓɓukan haɗin gwiwa guda biyu na musamman waɗanda aka keɓance su da takamaiman bukatunsu.

Zaɓin farko shi ne, “Yin abin da aka fi so,” yana samuwa ne ga dukkan masu siye da kuma masu tallace-tallace, yana ba da damar kamfanuka su yi amfani da bayanan farko, tare da tabbatar da cewa wadanda aka nufa da tallace-tallacen ya riske su.

Nau’i na biyu shi ne abin da Jumi’a ta kira da “Auction Private,” wanda aka samar musamman domin masu talla, yana ba da dama domin ƙaddamar da kamfen din wayar da kan abokan cinikayya ta Intanet da aka fi sani da ‘e-commerce’ akan farashi mai rahusa a kan mutum dubu da ya riska.

“Muna farin cikin bayyana tsarin shirin tallace-tallace a matsayin wata mafita da za ta kawo sauyi ga abokan aikinmu masu daraja. A Jumia, mun ci gaba da haɓaka ƙima a cikin tallan dijital, kuma wannan yana jaddada sadaukarwarmu. Ta hanyar shirin tsarin Tallace-tallace, muna neman ƙarfafa masu siyarwa da kuma masu tallace-tallace a duk faɗin Nijeriya, tare da ba su kayan aiki na ci gaba da kuma bayanan da aka yi amfani da su domin samun kyakkyawan sakamakon tallace-tallacensu,” in ji Massimiliano Spalazzi, Shugaban Jumia Nigeria.

Wannan ƙaddamarwa da Jumia ta yi wani bangare ne na dabarun shirin Jumia domin haɓaka kudaden shiga da haɓaka hanyarta ta samun riba. Tallace-tallacen Jumia yana a matsayi na uku (kuma na farko a Afirka) a bangaren bunkasa kudaden shiga na tallace-tallace na ‘Digital Ad Revenue Growth’ a cikin 2022 a cikin manyan masu talla a dijital 10, kamar yadda e-marketer – Inside Intelligence ta fitar.

Related Posts