Home » Moniepoint Za Ta Magance Matsalar Batun KYC Da Bankin Fidelity

Moniepoint Za Ta Magance Matsalar Batun KYC Da Bankin Fidelity

TECH Hausa ta labarto cewa; Bankin Moniepoint Microfinance, bankin da ke bada damar huldar kudi baki daya da sauran bankuna tare da kuma bada damar gudanar da ayyukan kasuwanci cikin sauki, ya sha alwashin cewa ba zai huta ba har sai ya tabbatar da cewa abokan cinikayyarsa na jin daɗin ƙwarewarsa wajen hulda da sauran bankuna.

Bayanai sun nuna cewa Bankin Fidelity, wani bankin kasuwanci na Nijeriya, ya toshe bankunan da suke sakar sama wato Intanet, kamar irin su OPay, Palmpay, Kuda, da Moniepoint saboda yadda wasu kwastomomi ba su sanya cikakkkun bayanansu wajen bude bankunan wanda aka fi sani da KYC (Know Your Customer) a takaice.

Wannan dalilin yasa bankin na Fidelity Bank ya toshe musayar kudade zuwa bankunan da ya hada da Moniepoint, Kuda, OPay, da PalmPay, kamar yadda wadansu majiyoyi da yawa da suke da masaniya kan lamarin.

A cewar wani rahoto na Techcabal, mako guda da ya gabata, ’yan tsirarun kwastomomi sun fara lura da cewa ba a sake sanya wadannan bankunan neobank a cikin jerin cibiyoyin hada-hadar kudi da aka amince da su a manhajar bankin Fidelity. Akalla majiyoyi biyar ne suka tabbatar da faruwar lamarin.

Wannan matakin da bankin Fidelity ya dauka ya sanya ya toshe wadannan bankunan na Intanet da TECH Hausa ta labarto a manhajarsu ta tura kudi da waya ya zuwa hada wannan rahoton. A yayin da bankin ya sanar da abokan cinikayyarsa cewa wannan hanin yana da alaƙa da haɓaka manhajarsa da ya yi, sai dai wasu mutane biyu da ke da masaniya ta kai tsaye game da lamarin da wasu majiyoyi daga wanda abin ya shafa, sun ba da labari na daban.

Da yake magana game da lamarin, Mista Bemigho Awala, shugaban sashen sadarwa na kamfanin Moniepoint Inc., ya ce tsaro na daya daga cikin muhimman abubuwan da Moniepoint take ba da muhimmanci, a don haka ma suna da tsarin tsaro nagartacce.

Awala, wanda yake magana a taron dandalin NITRA Fintech Forum a yau, ya ce kamfanin ya bude tattaunawa da tawagar Bankin Fidelity domin warware matsalolin.

Ya tabbatar wa abokan cinikinsa cewa Moniepoint za ta ci gaba da tabbatar da kare tsarin zambo.

Related Posts