Home » Airtel Ya Bada Tallafi Ga Cibiyar Bukatu Na Musamman A Legas

Airtel Ya Bada Tallafi Ga Cibiyar Bukatu Na Musamman A Legas

Kamfanin sadarwa na Airtel Nigeria, a karkashin shirinsa na ‘Touching Lives Initiative’, ya bada tallafin kayan aiki da dama ga Cibiyar Tallafawa masu bukatu na musamman, daya daga cikin masu cin gajiyar shirin na 7 a Unguwar Amukoko, dake Ajegunle a Legas.

Tawagar Airtel ta gabatar da shirin ne a harabar Cibiyar a ranar Talata, 24 ga Oktoba, 2023.

Misis Franca Nnedum, Cibiyar ta Fasaha da bukatu ta musamman, wasu masu sha’awa ne da juriya suka kafa ta inda suke gabatar da muhimman ayyuka da tallafi ga mutanen da suke da bukata ta musamman da dangoginsu.

Tafiyar ta Mrs. Franca, wanda gogayya ta samar da ita, ya kasance shaida mai ban sha’awa ga ƙarfin ruhun ɗan adam.

A ci gaba da jajircewar kamfanin na Airtel wajen tallafa wa daidaikun mutane da al’ummar da suke da bukata, kamfanin ya tantance bukatun cibiyar tare da daukar matakan da suka dace ta hanyar samar da kayan aiki masu amfani da za su taimaka wajen inganta rayuwar yara da matasa wadanda ke karbar magani da horarsar rayuwa a cibiyar.

Da yake jawabi a yayin mika kayayyakin tallafin, Mista Carl Cruz, shugaban kamfanin na Airtel Nigeria, wanda ya samu wakilcin Chika Obanor, daraktan ayyuka na yankin, ya bayyana aniyar Airtel na yin tasiri mai ma’ana a cikin al’umma a fadin kasar nan.

Related Posts