Home » Ecobank Ta Horas Da Daliban Sakandare Ilimin Fasahar AI Da Mutum-mutumi

Ecobank Ta Horas Da Daliban Sakandare Ilimin Fasahar AI Da Mutum-mutumi

Bankin Ecobank Nigeria, wanda yake reshe ne na kamfanin Ecobank Group, daya daga cikin manyan bankunan Afirka, tare da haɗin gwiwar kamfanin Opolo Global Innovation Ltd, ya soma shirin haɓaka ƙwarewar ilimin dijital a tsakanin ɗaliban Makarantar Trinity, dake Ojodu da Makarantar Harpers, dake Gbagada Phase 2, duk a cikin garin Legas a yayin bikin cika shekaru 10 na ranar Ecobank ta shekara-shekara.

Ranar ta Ecobank da ake kira da ‘Ecobank Day’ a turance, biki ne da aka kaddamar da shi a karkashin shirin tallafawa al’umma na bankin wanda Ecobank da ma’aikatansa ke ba da gudummawarsu ga al’ummarsu.

Shirin horaswar ya yi daidai da lokacin da bankin ya ƙaddamar da kamfen dinsa na ranar Ecobank na shekaru uku wanda aka ƙaddamar a rassan Ecobank 33 na Afirka.

Taken kamfen din shi ne ‘Sauya Afirka Ta hanyar Ilimi’. A shekara ta farko na shirin ya mai da hankali ne kan ilimin dijital domin samar da damarmaki ga yara da matasa domin su samu ƙwarewar a ilimin fasaha na zamani wanda za su buƙata domin ayyukan gaba.

Ecobank ya yi alkawarin gina cibiyoyin ilimin fasaha da aka fi sani da IT a turance har guda 33 a duk inda bankin yake a matsayin wani muhimmin sashe na ayyukansa na ranar Ecobank.

A nasa tsokacin kan ayyukan ranar Ecobank, Bolaji Lawal, Manajan Darakta na bankin Ecobank Nigeria, ya ce: “An yi hasashen yawan al’ummar Nijeriya zai kai miliyan 400 nan da shekarar 2050 kuma yana da matukar muhimmanci mu wadata matasanmu da ingantattun dabarun da za su iya amfani da su tare da saita su domin gudanar da ayyukan gobe.Muna cikin zamanin ci gaban fasaha cikin sauri tare da neman masu ƙwarewa a bangaren ilimin fasaha ga masu aiki. Muna alfahari da kasancewa wani ɓangare na bunkasa ilimin fasaha a Nijeriya. Ina so in gode wa abokan aikinmu wadanda suka sanya wannan rana ta zama gaskiya ga matasanmu”.

Misis Olajumoke Rowaye, Shugabar Makarantar Trinity, dake Ojodu ta ce “muna godiya ga Ecobank Nigeria bisa wannan karamcin. Ba mu Kwamfuta da horas da ilimi kan fasahar AI da mutum-mutumi (robotics) za su yi matukar taimakawa sosai wajen yin tasiri ga yaranmu.”

Har ila yau, Sunmisola Nwanze, Babban Malami a Makarantar Harpers, dake Gbagada Phase 2 a Legas ya ce, “Wannan haɗin gwiwa abin farin ciki ne. Wannan zai kara sanya mana sha’awar Ecobank. A bisa hakan, muna godiya da horar da yaranmu da kuka yi kan dabarun ilimin fasaha. ”

Ranar Ecobank ta tallafawa tare da kuma haɓaka abubuwa masu mahimmanci a kowace shekara tun daga 2013. Waɗannan su ne Ilimi ga matasa a Afirka (2013); Rigakafin cutar zazzabin cizon sauro (2014); Kowane ɗan Afirka ya cancanci kyakkyawar makoma (2015); Ilimin ICT a makarantu da inganta lafiyar mata (2016); Tsaftace ruwa (2017); Gidan marayu (2018); Ciwon daji (2019); Ciwon sukari (2020); Lafiyar kwakwalwa (2021) da kuma ilimin sanin kuɗi da yadda ake sarrafa shi (2022).

Related Posts