Home » 9mobile Ta Yi Bikin Cika Shekaru 15 Da Kafuwa A Nijeriya

9mobile Ta Yi Bikin Cika Shekaru 15 Da Kafuwa A Nijeriya

Tech Hausa ta labarto cewa; kamfanin ‘Emerging Markets Telecommunications Services (EMTS)’ dake gudanar da layin sadarwa na 9mobile, ta yi bikin cika shekaru 15 a Nijeriya, wanda hakan ke nuni da irin gagarumin ci gaba da kamfanin ta samu tafiyarsa na samar da ayyuka na musamman na sadarwa ga abokan hulda a fadin kasar.

Kamfanin wanda ya shiga harkokin kasuwancin sadarwa a Nijeriya a ranar 23 ga Oktoban 2008, duk da rugujewar kamfen din ‘0809ja’, kamfanin ya kasance kan gaba wajen kirkire-kirkire, tare da isar da sabbin hanyoyin sadarwa na zamani domin biyan bukatun kasuwanci ga daidaikun mutane.

A cikin shekaru 15 da suka gabata, 9mobile ya tabbatar da nagartarsa a matsayin kamfanin gaske na Nijeriya wanda ya shahara wajen tashe, bijiro da kirkire-kirkire, zama abin dogaro, da kuma fifita bukatun abokan cinikayya.

A tsawon tafiyarsa, kamfanin ya ci gaba da rungumar ci gaban fasaha, tare da tabbatar da cewa ayyukansa sun kasance a sahun gaba a masana’antar ta sadarwa.

Tun daga farkon fara ayyukansa wanda aka dogara kawai zuwa ga kiran waya har zuwa yanzu dake amfani da intanet cikin sauri, saukin hanyar ajiya ta Intanet, da kuma hanyoyin sadarwa na zamani, 9mobile ya ci gaba da daidaita kansa tare da biyan bukatun zamani na dijital.

Juergen Peschel, Shugaban 9mobile ya ce “Mun yi farin ciki da bikin cika shekaru 15, wannan wani muhimmin ci gaba ne da ke nuni da sadaukarwarmu domin samar da manyan hanyoyin sadarwa”.

Ya ci gaba da cewa; “nasararmu ta samu ne sakamakon abokan cinikayarmu masu aminci, abokan hulɗarmu, masu zuba hannun jari, masu sa ido, da kuma aiki tuƙuru na ƙwararrun ma’aikatanmu. Wasu daga cikin ma’aikatanmu sun kasance tare da wannan masana’anta tun daga farkon kafa ta har zuwa wannan shekarar da muke wannan bikin wanda wannan ya nuna irin goyon bayansu da jajircewarsu”.

“A yayin da muke waiwaye, muna jin daɗin kasancewamu a matsayin kamfanin Najeriya wanda ya kawo sauyi ga masana’antar sadarwa ta Nijeriya tare da sabbin kayayyaki, ayyuka, da mafita waɗanda ke ƙarfafa matasa, ƴan kasuwa, da ma dukkan sassa a faɗin ƙasar.” Ya ce.

Peschel ya jaddada cewa jajircewa da karfin kamfanin ya ta’allaka ne ga Nijeriya, wanda a cewarsa haɓakar kamfanin kyakkyawar shaida ce ta sauye-sauyen kamfanin, mai da hankali, da ƙarfin aiki a matsayin kasuwanci a yayin da yake amfani da ƙarfin fasaha domin sadar da fasahohi da ayyuka masu mahimmanci domin biyan bukatun abokan cinikayya.

A cikin shekaru 15 da suka gabata, 9mobile ya sami nasarori masu yawa, ciki har da fadada hanyoyin sadarwarsa, ƙaddamar da sabbin kayayyaki da ayyuka, da kulla dabarun haɗin gwiwa tare da shugabannin masana’antu.

Jajircewar kamfanin da yadda yake biyan bukatar abokan huldarsa da kwazonsa, ya sanya ya samu lambobin yabo da yawa da kuma karramawa a bangaren sadarwa.

“Muna alfahari da duk nasarorin da muka samu a tashin farko a cikin wannan masana’antar. Muna shirin ƙara karfafa ayyukanmu duk da ƙalubalen yanayin kasuwanci da ake fuskanta a kasar. Abubuwa da dama sun faru da mu na kalubale, amma za mu ci gaba da karfafa wa bisa nasarorin da muka samu a cikin shekaru masu zuwa,” in ji shi.

A kwanan nan ya ƙaddamar da shirin ‘The Hack’, wani shiri domin kanana da matsakaitan sana’o’i da aka fi sani da SME a turance wanda ke aiki a matsayin gudummawa ga ƙananan kamfanoni, wanda ya ratsa birane da harabar makarantun gaba da Sakandare.

Har ila yau, kamfanin ya bada gudummawa a bangaren ilimi, fasaha, da al’adu a karkashin shirin ‘9mobile Telecommunications Engineering Postgraduate Program (9TEPP)’. Sannan yana da lambar yabo ta Afirka a karkashin shirin ‘9mobile Prize for Literature’ ma’ana shirin wallafe-wallafe na 9mobile da ke inganta ilimin karatu da kuma ƙarfafa marubuta domin inganta sana’arsu a fadin Afirka da gasar daukar hoto.

Related Posts