Home » Bolt Ya Bude Sabuwar Cibiyar Direbobi a Legas

Bolt Ya Bude Sabuwar Cibiyar Direbobi a Legas

Kamfanin Bolt mai gwagwarmayar kasuwanci a Nijeriya a bangaren fasaha ya kaddamar da sabuwar cibiyar hada hadar tuki domin bunkasa kwarewar abokan huldarsa a fannin ayyukan da ya sa gaba.

Tech Hausa ta labarto cewa; cibiyar ta haɗakar direbobi za ta ƙara tallafawa tare da ƙarfafa dubun-dubatar abokan aikinta direbobi da ke samun kuɗi tare da Bolt a Legas.

CIbiyar wacce aka yi ta a lamba 11 Providence Street, Lekki Phase 1, cibiya ce ta direbobi da za ta haɓaka ingancin ayyukan direbobin da za su amfana ta wannan cibiya.

Cibiyar za ta inganta bai wa direbobi tallafi, hanyoyin sadarwa, damar horarwa, gina al’umma, warware matsaloli, gamsuwar direba, da kuma jinjina mai kyau da kuma taimakawa sabbin abokan hulda direbobi da za su hau hanya cikin sa’a daya ko biyu.

Bugu da kari, cibiyar za ta kasance wuri ajiyar abin da aka rasa ko aka bari inda fasinjoji za su iya karbar kayansu da aka manta a cikin motocin Bolt a yayin hawansu.

Yahaya Mohammed, shugaban gudanarwa na Bolt Nigeria, ya ce; “Wannan wani bangare ne na alkawurran da muka dade muna tanadi na saka hannun jari a ayyukanmu domin samar da ingantacciyar tallafi ga abokan aikinmu da kuma tabbatar da cewa sun ci gaba da bunkasa. Direbobi su ne jigon kasuwancinmu, kuma muna son ganin sun yi nasara kuma su haɓaka abin da suke samu. Mun kuma fahimci cewa kowane lokaci yana da muhimmanci kuma a koyaushe muna neman hanyoyin da za mu inganta ƙwarewar sabbi da daddadun direbobi domin samun mafi yawan lokacinsu akan hanya.

“Bolt yana da cibiyar tuki a Legas tun 2017, amma idan aka yi la’akari da ƙwararrun direbobinmu, mun himmantu wajen buɗe cibiyar tallafawa wacce za ta rika aiki, ta kuma tafi daidai da zamani da fasaha domin ƙarfafa yunƙurinmu na ci gaba da samar da lokaci da samar da wurin tallafa wa abokan aikinmu,” in ji Yahaya.

Sabuwar cibiyar ta direbobi ta Bolt za ta zama hanya mai sauri da dacewa ga abokan haɗin gwiwa a duk cikin garin Legas- inda za su iya yin rajista domin tuƙi ko yin tambayoyi game da manhajar ta Bolt.

Bolt ya ci gaba da aiki a kan cikakkiyar kwarewar direba da kuma ba da tallafin da direbobi ke buƙata domin tabbatar da cewa sun ci gaba da samun nasara a kasuwancinsu.

Kamfanin ya ce ya ci gaba da jajircewa wajen ganin ya aiwatar da shawarwarin da direbobi suke bayarwa dangane da kasuwancin.

Related Posts