Home » Sabbin Masu Amfani Da Manhajar X Za Su Soma Biyan Naira Dubu Daya

Sabbin Masu Amfani Da Manhajar X Za Su Soma Biyan Naira Dubu Daya

A yayin da yake maida hankali wajen yaƙar sakonnin ‘spam’, magudi, da ayyukan ‘bot’ a kan dandamalin na X, wanda aka fi sani da Twitter a da, ya sanar da ƙaddamar da sabuwar hanyar biyan kuɗi mai suna “Not A Bot”, inda ya nemi masu amfani da manhajar da ba a tantance su ba da su biya dala daya ($1) kwatankwacin naira dubu daya a shekara.

Wannan yunƙurin na X, wanda ya fara gwaji a ranar 17 ga Oktoba, 2023, an ƙirƙira shi ne musamman domin dakile tasirin ayyukan ‘bots’ da masu satar bayanai a yayin da ke tabbatar da ƙwarewar da ba ta dace ba ga masu amfani na gaske. Gwajin a halin yanzu yana aiki a New Zealand da Philippines.

Masu amfani da X a kasashen New Zealand da Philippines suna da bukatar tabbatar da lambar wayoyinsu domin bude asusu a manhajar X.

Sannan masu amfani da manhajar suna da damar da za su nemi shiga tsarin ‘Not A Bot’, wanda sai ka biya kudin shekara-shekara. Sai dai X ta ce kudin zai rika bambanta daga kasa zuwa kasa la’akari da kudaden kasar su.

Sannan idan ka biya kudin za ka iya yin rubutu, danna sha’awarka kan rubutu, maida martani, taya yada rubutu, da dai sauran su.

Wadanda kuma ba su biya kudin ba, ba za su samu wadancan damar ba. Damar da suke da shi kawai shi ne na karanta abubuwan da ake rubutawa daga sauran masu ta’ammuli da shafin.

Sai dai X ya ce wadanda suke amfani da manhajar a halin yanzu, wannan sabon tsarin ba zai shafe su ba.

Tsarin a cewarsa zai shafi sabbin masu bude asusun a manhajar ne.

Related Posts