Home » Sabon Shugaban Hukumar Sadarwa Ta Nijeriya, Aminu Maida Ya Soma Aiki Da Manufar Inganta Sadarwa A Kasar

Sabon Shugaban Hukumar Sadarwa Ta Nijeriya, Aminu Maida Ya Soma Aiki Da Manufar Inganta Sadarwa A Kasar

Aminu Maida (Dr.), sabon Mataimakin Shugaban Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC), ya ce zai daidaita tsarin hukumar wajen mayar da hankali don cimma alkawurran da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dauka na ‘sabunta fata’ da aka fi sani da ‘Renewed Hope’ domin ciyar da kasar gaba.

Maida, wanda ya yi magana da manyan jami’an hukumar a babban ofishin hukumar da ke birnin Tarayya Abuja a ranar Talata, ya ce akwai bukatar a tabbatar da cewa hukumar ta NCC ta mayar da hankali sosai wajen tabbatar da cewa dukkan ‘yan Nijeriya sun samu hanyoyin sadarwa mai sauki kuma abin dogaro.

Ya ce ta wani bangare shi ne domin tabbatar da “ingantacciyar hanyar bunkasa kayayyakin sadarwa a fadin Nijeriya”.

Sabon mai kula da harkokin sadarwa ya kuma jinjinawa tsofaffin shugabannin hukumar bisa rawar da suka taka wajen gina masana’antar sadarwar.

Dakta Aminu Maida ya ce, hanyar inganta hanyoyin sadarwa zai kasance daya daga cikin abubuwan da ya sa a gaba, da kuma tallafa wa manufofin gwamnatin tarayya da ma’aikatar sadarwa, kere-kere da tattalin arziki na zamani.

“La’akari da gaskiyar cewa mutane da yawa suna ƙara samun ilimin dijital tare da gudanar da ayyukansu ta Intanet a dukkanin abin da suke yi, kayan gudanar da aikin sadarwa suna samun matsuwa sosai. Kudurin Shugaba Tinubu ya jaddada bukatar gina hanyoyin sadarwa mai karfi wanda ba wai kawai zai saukaka hada-hadar kudi ta zamani ba har ma ya zama ginshikin gudanar da mulki ta intanet da sauran tsare-tsare na zamantakewa da tattalin arziki,” inji shi.

Ya ci gaba da cewa; “A saboda haka, za mu yi daidaita da wannan kuduri domin ƙara yawan shigar da layin sadarwa zuwa kashi 70 cikin 100 da kuma cimma kashi 90 cikin 100 na yawan al’umma nan da shekarar 2025. Don haka, muna buƙatar gina ingantacciyar masana’antar sadarwa tare da ingantaccen sabis (QoS), ingancin kwarewa (QoE) a matsayin madubin kallonmu wajen cimma manufarmu. Wannan kuma yana buƙatar mu magance batutuwa da yawa kamar ƙalubalen ‘Right of Way (RoW)’, tabbatar da tsaro na hanyoyin sadarwar mu, da sauransu. Dole ne a yi ƙoƙari domin inganta ayyukan sabis ta hanyar tabbatar da cewa NCC tana aikin da ya dace,” inji shi.

Ya ci gaba da cewa, a cikin tsare-tsare na Ministan ma’aikatar sadarwa da kirkire da tattalin arzikin zamani, an yi wani shiri na bai wa ‘yan Nijeriya miliyan uku tallafin sana’o’in zamani da kasuwanci, inda ya kara da cewa hakan zai bukaci hukumar ta tallafa wa Cibiyar Dijital Bridge (DBI) a matsayin cibiyar horar da dijital a matsayinta na cibiyar horaswa domin tafiyar da kudurin gwamnati kan karfafa matasa.

Shugaba Aminu Maida, ya kuma jaddada muhimmancin da yake akwai na sarrafa bakan da kuma amfani da shi wajen tallafawa tsarin haɗin kai na dijital da aka tsara, wanda ke da muhimmanci ga ƙaddamar da sabis ga gabaɗayan ‘yan Nijeriya da kasuwanci a cikin ƙasa.

Related Posts