Home » Bayan Shekaru 5: Mutum Miliyan 40 Ne Yanzu Ke Amfani Da Opay

Bayan Shekaru 5: Mutum Miliyan 40 Ne Yanzu Ke Amfani Da Opay

Tech Hausa ta labarto cewa; bayan shekaru biyar da kafa manhajar ajiya da cire kudi ta Opay mallakin kamfanin OPay Digital Services Limited, a yanzu haka mutum miliyan arba’in ne ke amfani da manhajar.

Hakan na kunshe ne a sanarwar da Opay ta turawa Tech Hausa a ranar Litinin 16 ga Oktoban 2023.

Opay ta ce labarinsu ba kawai kai wa adadin wadannan kwastamomi bane, a’a labarinsu na cike da labarai kala-kala, kulla alaƙa da abubuwa daban-daban wadanda suka taimaka wajen cimma wannan nasarar a yau. Opay ta ce; “Muna so mu sanya wannan kalmar ta “nagode” fiye da kalma ɗaya kawai; muna son ya zama nuni na gagarumin yabo da godiya da muke yi muku”, in ji su.

Ta kara da cewa; “OPay Digital Services Limited a ko da yaushe ya kasance mai himma domin yi muku hidima mafi kyau, kuma ci gaban da muka samu a yau ya sake tabbatar da sadaukarwar mu. Muna da matuƙar jindadi da samun ku a matsayin wani ɓangarenmu, kuma mun gane cewa abubuwan da muka cimma sun samu ne ta hanyar goyon bayan da muka samu daga gare su tare da kuma amincewar ku”, in ji sanarwar.

Opay ta ci gaba da cewa; kowacce hulɗa, da kowacce mu’amala ta kudi da aka yi da su ya nuna irin dogaro da amincewar da aka yi da su wanda suka ce hakan ya taimaka matuka wajen cimma nasarar su.

“Kun kasance masu karfafa mana da jan ragamarmu, kun kara mana ƙwarin gwiwa, kuma wannan dalilin ne yasa muke ƙoƙarin ingantawa tare da ƙirƙirar sabbin fasahohi” in ji su.

A karshe Opay ta jaddada cewa; a yayin da suke ci gaba, sun himmatu fiye da kowanne lokaci domin samar wa da masu amfani da su mafi kyawun ayyuka da gogewa. “Za mu ci gaba da saka hannun jari a fasaha, tsaro, da gamsuwar abokan cinikayya domin tabbatar da cewa haɗin gwiwarmu da ku ya kasance mai ƙarfi da lada kamar koyaushe”.

“A don haka, ga dukkanin abokan cinikinmu masu kima, a yayin da muke bikin godiya ga mutum miliyan 40, ku tuna da kalmarmu a kowanne lokaci ta “nagode” bisa yadda kuka ɗauki nauyin ba mu gudummawar ku, rikon amana, tare da haɗin gwiwa. Ba za mu iya yi ba in ba tare da ku ba”, suka karkare.

Related Posts