Home » Kamfanin Microsoft Zai Tallafawa Kananan Sana’o’i Miliyan 10 A Afirka Nan Da 2025

Kamfanin Microsoft Zai Tallafawa Kananan Sana’o’i Miliyan 10 A Afirka Nan Da 2025

Kamfanin Microsoft na son karfafawa kanana da matsakaitan masana’antu (SMEs) har guda miliyan 10 a Afirka nan da shekarar 2025.

Tallafin na Microsoft zai bada shi ta hanyar taimako, kayan aiki, tare da tallafin da suke da bukata wajen haɓɓakawa tare da fito da dabarun haɗin gwiwa domin bunkasa kasuwancinsu.

Me yasa wannan tallafin ke da muhimmanci? Bayanai sun nuna cewa kanana da matsakaitan sana’o’i sune kashi 90% na kasuwancin duniya.

A sakamakon haka ne, gogarman kamfanin ya sanar da haɗin gwiwa na shekaru biyar tare da Flurterwave domin cimma wannan.

Me yasa Microsoft ya zabi Flutterwave? Lillian Barnard, shugaban Microsoft na Afirka, ya ce yin hadin gwiwa da kamfanin dake sha’anin kudi na Afirka zai hanzarta samar da fasahohi da kirkire-kirkire wanda zai bunkasa ilimin dijital a harkar sha’anin kudi a nahiyar.

A matsayin wani ɓangare na haɗin gwiwar, Flutterwave za ta gabatar da hanyoyin da za a iya bibiya cinikayya a kasuwar Azure, ciki har da kananan da matsakaitan kasuwanci wanda zai ba da damar isa ga masu bukata.

Shugaban kamfanin na Flutterwave, Olugbenga Agboola, ya bayyana cewa, burin kamfanin shi ne yi wa biliyoyin ‘yan Afirka hidima ba tare da sun fuskanci wata matsala ba tare da kuma samar da ababen more rayuwa da za su saukaka musu wajen biyan kudi ga masu amfani da su a Afirka ko kuma a ko’ina a duniya.

Related Posts