Home » Daga Yanzu Masu Amfani Da Smartcash Za Su Iya Karbar Kudade Daga Kasashen Waje

Daga Yanzu Masu Amfani Da Smartcash Za Su Iya Karbar Kudade Daga Kasashen Waje

Smartcash Payment Service Bank (PSB) Limited, wanda reshe ne na kamfanin Airtel Nigeria, ya hada hannu da kamfanin Thunes, mai biyan bukatar masu huldar kudi da shi, zai bai wa kwastomomi damar karbar kudaden kasashen waje zuwa asusun ‘wallet’ dinsu.

Abokan cinikin Smartcash PSB za su iya karɓar kudi daga kasashen duniya zuwa asusun su ta lambobin wayar su.

A cewar Muyiwa Ebitanmi, shugaba kuma manajan Daraktan Smartcash PSB, ya ce haɗin gwiwar za ta taimaka wa masu fama da matsi ta hanyar bai wa mutanen da ke zaune a ƙasashen waje damar aika kuɗi da sauri ga ‘yan’uwansu a Nijeriya cikin sauƙi kuma ba tare da fargaba ba.

Ta hanyar sadarwar Smartcash, ana iya samun kuɗin nan da nan ba tare da an caje ka kudi mai tsada ga mai karɓa ba.

Sai dai wannan ba shi ne karon farko da wata manhajar kudi ta wayar salula ke yin haka a Nijeriya ba.

A watan Agustan 2023, MoMo PSB ta hada hannu da Saana Capital LLC, wata ma’aikatar musayar kuɗi ta duniya (IMTO), domin daidaita hanyoyin shigar kudi na ciki da waje a duk faɗin Afirka.

Mataimakiyar shugabar ci gaban cibiyar sadarwa, mai lura da Gabas ta Tsakiya da Afirka a Thunes Asma Ben Gamra, ta ce, “haɗin gwiwarmu da Smartcash PSB na da nufin sauƙaƙa hada-hadar kasuwanci ga miliyoyin ‘yan Nijeriya a Amurka, Turai da sauran ƙasashen waje, ta yadda za su saukaka musu wajen tallafawa iyalansu na gida.

Related Posts