Home » Za a ilmantar da ‘yan Nijeriya miliyan Uku a fannin fasaha

Za a ilmantar da ‘yan Nijeriya miliyan Uku a fannin fasaha

Bosun Tijani, ministan sadarwa, kirkire-kirkire, da tattalin arzikin dijital na Nijeriya (FMoCIDE), ya bayyana shirin ma’aikatar na horas da mutum miliyan uku masu koyo da kwararru a fannin fasaha nan da shekarar 2027.

Wannan horon zai haɗa da dabarun fasaha da kirkire-kirkire, ƙwarewa akan harkar fasaha, da kuma samun gogewa a fannonin fasaha daban-daban wanda ya ce hakan na daya daga cikin manufofin ma’aikatarsa.

Ministan ya ce shirin zai sauya fasalin fasahar Nijeriya tare da inganta ma’aikatar.

Mutum miliyan 1.5 daga cikin mutane miliyan 3 za a horar da su tare da tabbatar da cewa sun gudanar da ayyukansu a Nijeriya, a yayin da ake sa ran sauran za su yi fice da nuna hazaka a duniya ta hanyar samun damarmaki daga gida. Tare da gudanar da ayyukansu daga nan Nijeriya ba tare da sun je ko’ina ba.

Ministan ya ce tsarin yana da ginshiƙai guda biyar da ya hada da ilimi, tsare-tsare, kayayyakin gudanar da ayyuka, kirkire-kirkire, kasuwanci da jari, da kuma cinikayyah.

Mutane miliyan 3 da ake da manufar koyar da su ilimin fasaha yana wani bangare ne na koyar da ilimi daya daga cikin ginshiƙan da ake da su.

Sauran tsare-tsare dake cikin wannan ginshiƙin sun haɗa da samun kashi 95% na ‘yan Nijeriya masu ilimin fasahar zamani zuwa shekarar 2030 tare da sanya Nijeriya cikin kashi 25% na masu bincike a duniya.

Ministan har wala yau ya ce yana da niyyar haɓaka ƙa’idodi a fagage tara masu muhimmanci, wanda ya hada da bangaren tattara bayanai, sadarwa, AI, da kuma blockchain.

Related Posts