Home » Nijeriya Za Ta Sayi Sabon Tauraron Dan Adam Domin Inganta Tsaronta

Nijeriya Za Ta Sayi Sabon Tauraron Dan Adam Domin Inganta Tsaronta

Hukumar binciken sararin samaniya wacce aka fi sani da NASRDA, ta sanar da shirin mallakar wani tauraron dan adam mai karfin daukar hoto domin ya taimaka wajen gano matsalolin da ake fuskanta, nuna inda ‘yan bindiga suke, tare da kuma ba da sanarwar yunkurin da ‘yan ta’adda ke yi.

Darakta Janar na hukumar ta NASRDA, Halilu Shaba wanda Daraktan Cibiyar Bunkasa Fasahar Tauraron Dan Adam (CSTD), Dr Sadiq Umar ya wakilta ne ya bayyana hakan a wani jawabin shekara-shekara a karo na 7 da ya gabatar na Cibiyar Injiniyoyi ta Nijeriya (NISEng).

Me yasa hukumar ke son sayen sabon tauraron dan adam? A cewar hukumar, tauraron dan adam na kasar a halin yanzu, wato Sat X, ba za a iya amfani da shi ba wajen magance matsalolin rashin tsaro ba saboda yana isar da hotuna ne marasa inganci kawai.

“Kuna iya tantancewa ta hanyar amfani da mita 0.5 zuwa 1 kuma ba mu da kayayyakin da zai iya daukar mai karfin wannan.”

Me yasa gwamnati ke son daukar wannan matakin? Ba sabon abu ne cewa rashin tsaro na daya daga cikin manyan kalubalen da yake fuskantar Nijeriya. Barazana da dama da suka hada da ta’addanci, hare-haren ‘yan bindiga, rikicin kabilanci da na addini, da kuma aikata laifuka, sun addabi kasar shekaru da dama.

Kyakkyawan tauraron dan adam, kamar yadda Shaba ya jaddada, zai ba da damar tattara bayanai domin kula da muhalli, hasashen yanayi, tsaro na intanet, tare da samar da ingantattaun bayanai domin yadawa. A baya, tauraron dan adam na Nijeriya yana da matukar muhimmanci wajen kula da abin da ka iya biyo bayan ibtila’i da kuma lura da ibtila’o’i kamar ambaliyar ruwa, malalar mai, da gobarar daji.

Me muke bukata a yanzu? A cewar Shaba ya ce kasar na da bukatar tauraron dan adam na ‘Synthetic Aperture Radar’ wanda zai iya gani ta cikin gajimare da daddare.

Related Posts