Home » Wani kamfani mai zaman kansa zai zuba jarin dala miliyan 500 a Afirka a bangaren kimiyyah da fasaha

Wani kamfani mai zaman kansa zai zuba jarin dala miliyan 500 a Afirka a bangaren kimiyyah da fasaha

Kamfanin Alterra Capital Partners ya tara dala miliyan 140 a tashin farko na asusunsa, inda yake harar tara dala miliyan 500.

Asusun, wanda ake sa ran zai zuba jari a fannin sadarwa, fasaha, dabaru, kiwon lafiya, bangaren amfani da kayayyaki na yau da kullum, da kuma bangaren saye da sayarwa, inda ya samu goyon bayan Aliko Dangote, David Rubenstein, da kuma Bill Conway a matsayin masu hannun zuba jari.

Sauran masu saka hannun jari a cikin asusun sun hada da Norfund AS, Standard Bank Group Ltd., International Finance Corp., Deutsche Investitions- und Entwicklungsgesellschaft GmbH na Jamus, da asusun AfricaGrow na Allianz SE.

A yayin da ya fice daga nahiyar, kamfanin Alterra Capital Partners ya fara aiki a matsayin mai bada shawara ga asusun Afirka na Carlyle. Daga cikin kudaden dake cikin wannan asusu sun haɗa da hannun jarin dala miliyan 147 a Bankin Diamond da J&J Transport.

“Wannan lokaci ne da ya dace domin sanya kuɗi a yi aiki a Afirka, domin yawancin jigogin harkokin kasuwanci masu muhimmanci a yanzu suna ba da damar saka hannun jari masu kyau. Misali, kalubalen rashin wutar lantarki a fadin Afirka ya ba da damar saka hannun jari a hanyoyin samar da wutar lantarki masu zaman kansu, a yayin da sauye-sauye fasaha ke ci gaba da tafiyar bangaren dijital na Afirka cikin hanzari,” in ji Sangudi.

Per Sangudi ya ce, kamfanin ya yi nasarar mayar da dala miliyan 600 ga wadanda suka zuba hannun jarinsu, inda ya fice daga kamfanoni shida, ya kuma zuba hannun jari na kusan dala biliyan 1 a kamfanoni 23.

Manyan kamfanoni masu zaman kansu ko dai sun rage hannun jarinsu na Afirka ko kuma sun fice daga nahiyar baki daya, amma Carlyle tana daidaita dabarunta domin tunkarar yanayin kasuwanci na musamman.

Kamfanin ya ce zai zuba kashi 50 cikin 100 na kudadensa ga kamfanonin da ke samar da kudaden shigarsu a daloli, domin ba ya son fadawa fargabar faduwar darajar kudi a nahiyar.

Related Posts