Home » Wa ya kamata ya mallaki wayar Tecno POP 8?

Wa ya kamata ya mallaki wayar Tecno POP 8?

TECH Hausa tana mai gabatar muku da wayar Tecno Pop 8, wato wayar hannu mai cike da saukin kudi wacce ke dauke da abubuwa da dama a kanta.

Bari mu yi nutso mu bincika muhimman bayanai dangane da wayar hannu ta Tecno Pop 8 da dalilan da ya sa na’urar ta yi fice a tsakanin sa’o’inta.

Tecno Pop 8 tana da ƙarfi ta Unisoc T606 chipset, wanda aka gina akan tsarin 12nm. Octa-core CPU ɗin ta, ya ƙunshi 2 × 1.6 GHz Cortex-A75 da 6×1.6 GHz Cortex-A55 cores, yana daukar ingantattun ayyuka da yawa a lokaci a yau da kullum.

Ɗaya daga cikin fitattun fasalinta shi ne tana da fadin inci 6.6. Tare da girman sikirin mai ban sha’awa da ya kai kashi 84.6%, yana bayar da kayattaccen hoto a yayin kallo.

Yana da karfin ƙirar pixel 720 x 1612 da 20:9 idan aka raba, wanda zai iya bayar da ƙimar pixel kusan 267 ppi, wanda wannan ke tabbatar da karfi da nagartar da hoto zai ba ka a dukkanin ayyukanka.

Wayar Tecno Pop 8 za ta iya dacewa ga mai amfani da shafukan sada zumunta da ya hada Facebook, Tiktok, WhatsApp, Twitter (X a yanzu), Instagram da sauran su wajen gudanar da ayyukansa.

Kuma za ka iya daukar hoto da ita mai kyau musamman idan ta samu haske sosan gaske.

TAKAITACCEN BAYANI AKAN WAYAR TECNO POP 8

SIM: Guda biyu ake sanya ma ta.

NETWORK: tana da karfin GSM / HSPA / LTE

OPERATING SYSTEM: Android 13 (Go edition) ce.

CHIPSET: Unisoc T606 (12 nm)

CPU: Octa-core (2×1.6 GHz Cortex-A75 & 6×1.6 GHz Cortex-A55)

MEMORY: 128GB, 4GB RAM

Tana da girman: 6.6 inches, 104.6 cm2 (~84.6% screen-to-body ratio), 720 x 1612 pixels, 20:9 ratio (~267 ppi density)

KYAMARAR baya tana da 13 MP, f/1.8 (wide), 1.12µm, AF, 0.08 MP, (depth)

KYAMARAR BAYA tana da 8 MP

TANA DA FITAR DA MURYA SOSAI: domin lasifika biyu gare ta.

3.5mm jack: Yes

Sannan tana Fingerprint (a gefen wurin kashe wayar).

BATIRI DINTA: Li-Po, 5000 mAh, da ba a cirewa.

YADDA TAKE CAJI: tana caji a 10W ta hanyar karfaffar cajar da aka samar mata.

FARASHINTA A NIJERIYA: yana kai wa daga naira dubu 90 zuwa 100.

Related Posts