Home » NCC Ta Shawarci Yan Najeriya Su Gaggauta Goge Wasu Manhajojin a Na’ura su

NCC Ta Shawarci Yan Najeriya Su Gaggauta Goge Wasu Manhajojin a Na’ura su

Hukumar Kula da Harkokin Sadarwar ta Najeriya ta gano wasu abubuwan da ka iya kawo tsaiko ga ‘ya kasa a kan manhajar Google Chrome. A cewar hukumar, irin wadannan manhajoji na bin diddigin duk wasu shafuka da mai amfani dasu ke bi.

NCC ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafin yanar gizo na hukumar.
Manhajojin guda biyar da NCC tace a gujewan sune kamar haka.
1.McAfee Mobile
2.Netflix Party/Netflix Party 2
3.Full Page Screenshot Capture Screenshotting
4.FlipShope Price Tracker Extension
5.AutoBuy Flash Sales
NCC ta yi gargadin cewa, duk da akwai mutum sama da miliyan 1.4 dake amfani da manhajojin, duk da haka akwai hadarori da ke tattare dasu idan ba a kula ba.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, NCC ta ce akwai manhajojhi da yawa da Google suka cire a ma’ajiyar manhajoji Web Store, to amma abu ne mai wahala iya tsaftace kafar ta yanar gizo. A bangare guda, NCC ta shawarci masu amfani da wayoyin hannu da sauran abubuwan zamani da su ke karatun ta natsu kafin sauke manhaja a na’ur’rinsu.

Ana amfani da Chrome Extensions a na’urorin teburi da na tafi da gidanta, kana ana amfani da irin manhajojin da NCC ke gargadi a kai a wayoyin hannu.

Related Posts