Home » Banki Kuda Sun Tafka Asara Naira Biliyan 6

Banki Kuda Sun Tafka Asara Naira Biliyan 6

Shahararren bankin nan dake aiki a yanar gizo Kuda sun tafka Asara kudi wanda yawan shi ya kai Naira biliyan shida a shekarar 2021 wani rahoto da shafin Techcabal suka wallafa ya nuna kamfani yayi asara 2021, kamfanin ya yi asarar ₦6,092,554,866 ($14,214,681),a shekarar 2021 kashi 602% ya karu daga asarar ₦868,062,000 ($2,025,295) da ya yi a shekarar 2020.


Rahoton kudi ya nuna cewa kudaden shiga na kamfanin ya karu da kashi 4,315% daga ₦72,649,000 a shekarar 2020 zuwa ₦3,207,177,570 a shekarar 2021. Sai dai bayan an cire duk wani kudi, kamfanin ya rufe shekaran ne da asara mai yawa, tare da hasarar bashi da yawa.


Ana ganin bashin da Kuda ke bayarwa shine ya jawo musu wannan babban asarar da sukayi, sai dai tuni banki sun dakatar da bayar da bashin da sukeyi wa abokan hulɗar su.

Related Posts